Kai Tsaye: Yadda ake bikin mika sandar sarautar Zazzau ga sabon Sarki
Bayan sanar da sabon Sarkin Zazzau da Gwamna Nasir El-Rufai yayi, a ranar 9 ga watan Nuwamba ne yake mika masa sandar sarautar kasar Zazzau.
Ku biyo Legit.ng inda za ta dinga kawo muku abinda ke faruwa a filin Alhaji Muhammadu Aminu kai tsaye.
Gwamna yana jawabi ga manyan baki da jama'ar da suka samu hallara
Malam Nasir El-Rufai yana jawabin mika godiya tare da jan hankali ga jama'ar da suka samu halartar bikin mika sandar mulkin.
Gwamna ya mika wa Sarkin Zazzau sandar mulki
Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya mika sandar sarautar ga sabon Sarkin Zazzau. sabon Sarkin kuma ya dauka rantsuwar aiki a take
Bidiyon yadda jami'an tsaro a filin wasa na Muhammadu Aminu
Jami'an tsaro suna kokarin gyarawa tare da kimtsa mutane a yayin da manyan baki suke karasowa.
Gwamna El-Rufai ya isa filin wasa na Muhammadu Aminu
Gwamna Malam Nasir El-Rufai tare da sabon Sarki, Ambasada Ahmad Bamalli.
Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng
Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng