Kaduna: An sake tsintar gawar matasan 'yammata biyu a Kurmin Mashi a karo na uku

Kaduna: An sake tsintar gawar matasan 'yammata biyu a Kurmin Mashi a karo na uku

- Batun tsintar gawar matasan 'yammata a unguwar Kurmin Mashi da ke Kaduna na neman zama ruwan dare

- Ana zargin cewa maza da aikata fyade a kan kananan 'yammatan sannan su faki ido su jefar dasu bayan sun mutu

- Hafsat Baba, kwamishiniyar walwala da cigaban al'umma a jihar Kaduna ta roki kwamishinan 'yan sanda ya taimaka wajen bankado masu aikata wannan barna

A karo na biyu a cikin wannan shekarar, an sake tsintar gawar matasan 'yammata biyu da mutanen ba'a san ko su waye ba suka jefar a unguwar Kurmin Mashi da ke cikin garin Kaduna.

Batun tsintar gawar mata masu kananan shekaru da kuma matasa ya jefa tsoro, fargaba, da rudani a zukatan mazauna yankin Kurmin Mashi.

Kwamishiniyar ma'aikatar walwala, jin dadi, da cigaban al'umma a jihar Kaduna, Hafsat Baba, ta bayyana fushi da damuwarta a kan lamarin.

Hafsat ta bukaci kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, CP Muri Umar, ya yi amfani da jami'ansa domin bankado masu aikata wannan mummunar barna.

Ta bayyana cewa ya kamata rundunar 'yan sanda ta kawo karshen faruwar irin wannan abun takaici da ban haushi.

Ana zargin cewa maza ne ke fakar ido su jefar da gawar 'yammatan bayan sun yi musu rajamu wajen aikata fyade.

"Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnatinmu ke kokari tare da bullo da sabbin matakai domin inganta rayuwar yara Mata.

KARANTA: Abubuwa muhimmai masu ƙayatarwa game da Kamala Harris, mataimakiyar Biden

"Dole a kawo karshen wannan ta'addanci da yake neman gurbin zama a cikin wannan unguwa.

"Kwatankwacin irin hakan ya taba faruwa a lokacin da aka saka dokar kulle sakamakon bullar annobar korona. Har yanzu wadannan 'yan ta'adda na cigaba da cin karensu babu babbaka. Abin takaici ne, kuma ya zama dole a dakatar da su.

Kaduna: An sake tsintar gawar matasan 'yammata biyu a Kurmin Mashi a karo na uku
Kaduna: An sake tsintar gawar matasan 'yammata biyu a Kurmin Mashi a karo na uku
Asali: Getty Images

"Hakan na nuna cewa yaranmu Mata basu da tsaro Kenan a unguwanninsu. Ya zama wajibi jami'an tsaro su tashi haikan domin kawo karshen lamarin.

"Ina Kira ga kwamishinan 'yan sanda na jihar Kaduna, CP Muri Umar, ya taimaka mana wajen bankado masu aikata wannan mummunar barna," a cewar Hafsat.

KARANTA: Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi martani hade da shagube a kan tsine mata a Masallatai

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhamed Jalige, ya tabbatar wa da manema labarai batun tsintar gawar karamar yarinya.

Kafin faruwar hakan, an taba tsintar gawar wata yarinya mai shekaru 6 a wata makabarta da ke Kurmin Mashi.

Ana zargin cewa yarinyar ta rasa ranta ne sakamakon fyade da maza da yawa suka aikata a kanta.

Kazalika, a 'yan watannin baya kadan da suka gabata, an taba tsintar gawar wata yarinya mai shekaru 6 a wani Masallaci da ke unguwar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng