'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun kashe jami'ai biyu, yashe ma'adanar makamai

'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun kashe jami'ai biyu, yashe ma'adanar makamai

- Har yanzu batagari a jihar Edo na jihar na cigaba da cin karensu babu babbaka tun bayan rikicin da ya balle sakamakon zanga-zangar ENDSARS

- A daren ranar Litinin ne wasu 'yan bindiga suka kai hari wani ofishin 'yan sanda a jihar tare da yashe ma'adanar makamai

- 'Yan bindigar sun wulla sinadari mai fashewa tare da lalata wani sashe na ginin ofishin 'yan sandan

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kai hari ofishin 'yan sanda da ke karamar hukumar Igueben a jihar Edo tare da kashe jami'ai biyu; Insifekta da Konsitabul.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu jami'an 'yan sanda da dama sun samu raunuka, sannan kuma 'yan bindigar sun kwashe makaman ofishin 'yan sandan.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta ware Dangote daga dokar rufe iyakokin kasa

'Yan bindigar sun fara wulla wani sinadari mai fashewa zuwa cikin ofishin 'yan sandan a harin da suka kai da misalin karfe 8:00 na daren ranar Litinin.

'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun kashe jami'ai biyu, yashe ma'adanar makamai
'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun kashe jami'ai biyu, yashe ma'adanar makamai
Asali: UGC

Bayan sun tarwatsa wani bangare na ofishin 'yan sandan, 'yan bindigar, wadanda ake zargin 'yan fashi ne, sun samu damar shiga ofishin tare da yashe ma'adanar makaman ofishin.

DUBA WANNAN: Ba haka bane Farfesa; Shehu Sani ya ci gyaran Zulum a kan sababin fara yakin Boko Haram

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an adana gawar jami'an 'yan sandan a dakin ajiyar gawa.

Sai dai, Premium Times ta rawaito kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, na cewa babu jami'in da ya rasa ransa sakamakon harin, sai dai akwai wadanda suka samu raunuka.

Har yanzu al'amura basu daidaita ba a jihar Edo tun bayan rikicin da ya barke sakamakon zanga-zangar ENDSARS.

Legit.ng Hausa ta wallafa cewa wata kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar babban bankin Najeriya (CBN) na rufe wasu asusun banki 19 mallakar wasu daidaikun mutane da kamfanonin da aka gano cewa suna da alaka da zanga-zanagar ENDSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng