IPOB na yunƙurin sake haddasa yaƙin basasa a Nigeria - Gwamnonin Kudu maso Gabas

IPOB na yunƙurin sake haddasa yaƙin basasa a Nigeria - Gwamnonin Kudu maso Gabas

- Gwamnonin kudu maso gabas sun gudanar da wani taro tare da Gwamna Wike kan ayyukan kungiyar IPOB a jihar Ribas

- Gwamnan ya yi zargin cewa IPOB na shirin haddasa matsala a Najeriya

- Gwamna David Umahi ya ce kungiyar IPOB bata da goyon bayan shugabannin Igbo

Gwamnonin yankin kudu maso gabas sun zargi haramtaciyyr kungiyar nan ta Indigenous People of Biafra (IPOB), da kokarin haddasa sabon yakin basasa a Najeriya.

Gwamnonin sun yi zargin ne a daren ranar Lahadi, 8 ga watan Nuwamba, bayan sun gudanar da wani taro tare da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.

KU KARANTA KUMA: INEC: Yakubu zai mika ragamar mulki ga mukaddashin shugaba a ranar Litinin

Shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, David Umahi, wanda ya yi magana a madadin gwamnonin, ya yi gargadin cewa mutanen Igbo su yi hankali da mambobin IPOB.

IPOB na yunƙurin sake haddasa yaƙin basasa a Nigeria - Gwamnonin Kudu maso Gabas
IPOB na yunƙurin sake haddasa yaƙin basasa a Nigeria - Gwamnonin Kudu maso Gabas Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa sun yanke shawarar ziyartan jihar Ribas domin tabbatar da ikirarin da ake a soshiyal midiya wanda ke zargin cewa ana kashe yan Igbo a jihar.

Umahi ya bayyana cewa ziyarar da suka kai jihar ya nuna cewa ikirarin cewa ana kashe yan Igbo karya ne, jaridar The Nation ta ruwaito.

Gwamnan na jihar Ebonyi ya yi kira ga yan Igbo da su nesanta kansu daga IPOB. Ya ce shugabannin Igbo na adawa da matsayar IPOB.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin CBN: Fadar shugaban ƙasa ta magantu kan garƙame asusun masu zanga zanga

A wani labari na daban, mun ji cewa akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi zai sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Majiyoyi sun fada ma jaridar The Nation cewa Umahi na iya sanar da ficewarsa daga PDP, jam’iyyar da a cikinta ya lashe zaben gwamna sau biyu.

Jam’iyyar APC reshen jihar ta bugi kirji a ranar Lahadi game da shirin sauya shekar gwamnan, inda ta bayyana shi a matsayin ci gaba mai kyau.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel