Hukuncin CBN: Fadar shugaban ƙasa ta magantu kan garƙame asusun masu zanga zanga

Hukuncin CBN: Fadar shugaban ƙasa ta magantu kan garƙame asusun masu zanga zanga

- Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi martani a kan garƙame asusun masu zanga zangar EndSARS da CBN yayi

- Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya ce dole ne wadanda suka jagoranci zanga zangar wanda ya zama rikici su biya bashin abunda suka aikata

- Bankin CBN dai ya daskarar da asusun wasu mutane 20 da ke da nasaba da daukaka zanga zangar ta EndSARS wanda bata gari suka karbe a wasu yankunan kasar

Fadar Shugaban kasa ta ce duk wadanda suka bari zanga zangar #EndSARS da aka yi kwanan nan ya zama rikici da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi a kasar sai sun biya bashin abunda suka aikata.

Garba Shehu, babban mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kafofin watsa labarai, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayinda ya bayyana a shirin Channels TV.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa babban bankin Najeriya ta daskarar da asusun mutane 20 da suka jagoranci zanga zangar #EndSARS yayinda aka hana wata da ta daukaka gangamin, Modupe Odele, fita kasar waje a makon da ya gabata.

Har ila yau hukumar kula da shige da fice ta kwace fasfot dinta.

KU KARANTA KUMA: Garƙame asusun bankuna: Ana shirin fara sabuwar zanga zangar #EndSARS

Hukuncin CBN: Fadar shugaban ƙasa ta magantu kan garƙame asusun masu zanga zanga
Hukuncin CBN: Fadar shugaban ƙasa ta magantu kan garƙame asusun masu zanga zanga Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Da aka tambaye shi ko ubangidansa na sane da ci gaban, Shehu ya ce lamarin ya isa teburin Shugaban kasar, inda ya bayyana cewa dole masu zanga zangar su fuskanci doka.

Ya ce: “Kasar nan shugaba daya ne da ita sannan kundin tsarin mulki daya ne da ita. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke rike da gwamnati. Lamarin ya sauka a teburinsa.

“Mun kasance kasa da ke jagoranci da doka. Akwai kundin tsarin mulki – karkashin sashi na 33 – cewa karara ya baiwa al’umma yancin yin zanga zangar lumana amma idan zanga zangar lumana ya zama rikici, da sace sace, akwai bukatar ayi aiki da doka da oda.

“Kowa ya ga tarin sace sace da aka yin a kayayyakin gwamnati da masu zaman kansu musamman a Lagas, Calabar, Filato, Taraba da wasu jihohi, harma da babbar birnin tarayya.

“A yanzu, ya zama dole a bari dokar kasa ta yanke hukunci, ta yi hukunci kan barnar da aka yi ta bangaren kowanene.

“Ba wai ina magana musamman a kan fitattu ko wadanda suka daukaka ta ba amma dai an yiwa kasar nan ba daidai ba kuma dole mutane su shirya girbe abunda suka shuka.”

KU KARANTA KUMA: Ka gaggauta yin zaɓen shuwagabannin APC ko ka sauka daga riƙon ƙwarya - Marafa ga Buni

Ya kara da cewa wasu yan siyasa, wadanda suka daukaka zanga zangar #EndSARS ciki harda na PDP “su fito su yi Allah-wadai da barnar da zanga zangar ya haddasa a bainar jama’a.”

A gefe guda, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi zargin cewa masu daukaka zanga zangar EndSARS na so su yi amfani da shi ne wajen sauya gwamnati.

Dan majalisar a yayin wata hira da jaridar Daily Trust, ya yi ikirarin cewa wasu manyan yan Najeriya ne ke daukar nauyin zanga zangar EndSARS domin kaskantar da arewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng