Hotuna daga wurin shirye-shiryen mika sandar sarautar Zazzau
- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sanar da nadin Ambasada Ahmad Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19
- Bayan nan, an saka ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2020 da ya zamo ranar mika sandar sarauta ga sabon Sarkin
- Shirye-shirye sun kankama a filin Alhaji Muhammadu Aminu, wanda aka fi sani da filin Polo a Zaria
Bayan kasar Zazzau ta yi sabon sarki, Ambasada Ahmed Bamalli, wanda shine a da magajin garin Zazzau, za a mika masa sandar sarautar kasar a ranar 9 ga watan Nuwamba.
Kamar yadda katin gayyatar da Legit.ng ta gani ya nuna, za a yi taron a filin wasan Polo wanda ake kira da filin Alhaji Muhammadu Aminu da ke karamar hukumar Sabon gari.
Za a fara taron da karfe 10:00 na safiyar ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamban 2020.
Ga wasu daga cikin hotuna daga fadar Mai martaba sarkin Zazzau da kuma filin Alhaji Muhammadu Aminu, wanda aka fi sani da filin Polo a Zaria.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa

Asali: Twitter

Asali: Twitter
KU KARANTA: Kyawawan hotunan matar matukin adaidaita da ta haifa 'yan 5

Asali: Twitter
A wani labari na daban, babbar kotun jihar Kaduna da ke zama a Dogarawa, Sabon Gari a jiya ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 5 ga watan Nuwamban 2020 domin yanke hukunci a kan bukatar dakatar da sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Bamalli daga bayyana kansa a matsayin Sarkin Zazzau.
Amma kuma, lauyan sabon sarkin, Mahmoud Abubakar Magaji (SAN), ya kalubalanci ikon kotun na sauraron shari'ar, Daily Trust ta wallafa.
Magaji ya ce tunda akwai kalubale a kan iko, ana tsammanin kotun ba za ta dauka wani mataki ba har sai an warware wannan matsalar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng