Kyawawan hotunan matar matukin adaidaita da ta haifa 'yan 5

Kyawawan hotunan matar matukin adaidaita da ta haifa 'yan 5

- Hotunan wata matar matukin adaidaita sahu tare da 'yan biyar da suka haifa sun karade kafafen sada zumunta

- Ndidi Odo mai shekaru 32 a duniya ta haifa yaran a jihar Anambra bayan tana da yara hudu rayayyu

- Wani hamshakin dan kasuwa ne ya biya kudin asibitinsu tare da daukar nauyin karatunsu har jami'a

Ndidi Odo mace ce mai shekaru 32 a duniya kuma matar matukin adaidaita sahu ce wacce hotunanta ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani.

Ba komai ya janyo cece-kuce a kan hotunanta ba da ya wuce 'yan biyar da ta haifa da suka hada da yara maza uku da mace daya.

Sunansu shine: Akachukwu, Chiemelie, Chidiomimi, Chinweolu da Ezinwanne.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa, Ndidi da mijinta mai suna Abuchi Odo 'yan asalin Okpaligbo-Ogu da ke Nsukka a karamar hukumar Enugu.

Sun haifa 'yan biyar a 2018 a asibitin God's Mercy da ke Obiuno a Otolo Nnewi, jihar Anambra.

Ma'auratan suna da yara hudu tun kafin su haifa 'yan biyar din.

Nnewi wani fitaccen dan kasuwa ne kuma mai taimakon jama'a. Ya biya kudaden asibitin 'yan biyar sannan ya dauka alwashin daukar nauyin karatunsu har zuwa jami'a.

Babu tabbaci a kan lokacin da aka dauka hotunan. Daya daga cikin mambobi a kungiyar jin kan ne ya ziyarcesu sannan ya wallafa hotunansu.

Kyawawan hotunan matar matukin adaidaita da ta haifa 'yan 5
Kyawawan hotunan matar matukin adaidaita da ta haifa 'yan 5. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci

Kyawawan hotunan matar matukin adaidaita da ta haifa 'yan 5
Kyawawan hotunan matar matukin adaidaita da ta haifa 'yan 5. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Kyawawan hotunan matar matukin adaidaita da ta haifa 'yan 5
Kyawawan hotunan matar matukin adaidaita da ta haifa 'yan 5. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kotu ta umarci jihar Kogi da ta biya korarren mataimakin gwamna N180m

A wani labari na daban, ministocin kudu maso yamma da aka umarta da su koma jihohinsu na gado saboda rikicin zanga-zangar EndSARS sun gabatar da rahoto ga majalisar zartarwa ta tarayya.

A rahoton da suka gabatar a ranar Laraba da safe, sun bukaci a yi bincike mai tsanani a kan harbin da sojoji suka yi a Lekki Toll Gate, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda rahotonni suka gabata, wasu mutane masu kayan sojoji sun iso Lekki Toll Gate ana tsaka da zanga-zanga, inda suka fara harbe-harbe, wanda hakan yayi sanadiyyar watsa masu zanga-zangar da dama, wasu kuma suka tsere, garin haka suka ji munanan raunuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel