Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa

Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa

- Mansurah Isah ta yi wa 'yan fim tonon silili, har da zargin madigo, inda tace kowa mai zunubi ne kuma Allah ne mai yafiya

- Jarumar ta bayyana zargin a shafinta na Instagram, bayan bayyanar hotunan Rahama Sadau wadanda suka janyo cece-kuce

- Ta yi wallafar ne bayan jaruman Kannywood sun yi ta bidiyo suna tsinewa Rahama Sadau, da hijabai a jikinsu

Tun bayan bayyanar hotunan Rahama Sadau, wadanda suka kawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani, mutane da dama musamman 'yan fim suka yi ta yin bidiyo suna la'antarta, har da masu hawayen takaici da bakinciki.

Kwatsam sai ga jaruma Mansura Isah ta yi wata wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram,mai cike da tonon silili, wacce ta harzukar da wasu daga jaruman fim din.

KU KARANTA: A raba ni da shi, gagarumin mashayi ne kuma yana dukana - Matar aure ga kotu

Mansurah Isah ta ce: "Wallahi da ban so yin magana ba, amma kun sa nayi. Wannan shirmen ya isa haka. Na ga wata da ta fito daga Police station kwanan nan tana wa'azi, mtsww.

"Wata da ta wallafa nonuwanta tana rawa a status ita ma tana wa'azi, wata da kowa ya san karya ce ('Yar Madigo) ita ma tana wa'azi. Kun gani ko, dukkaninmu masu zunubi ne, sannan mun fi tsoron mutane a kan tsoron Allah a zuciyar mu, amma za mu fito kafafen sadarwa muna nuna na Annabi ne.

Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa
Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa. Hoto daga @Mansurah_Isah
Asali: Instagram

"Kowacce in za ta yi magana sai ta saka Hijabi, wa ku ka yaudara? Ku je ku duba shafukansu ba saka Hijabi suke ba. Allah na kallonmu duka, shin duniya ce za ta yi muku hisabi?

"Dukkan ku kun samu wata dama ce ta fito da abinda ya ke cikin zuciyarku. A gurin Allah ne kadai zan nemi yafiya, kuma shi kaɗai zan yi wa kuka a ɓoye ko a fili a lokacin da na san na aikata laifi kuma na san cewa ban yi daidai ba.

"Wannan ya isheni ishara, ALLAH YA NA SON mai neman gafararsa koda sau nawa zai aikata laifi kuma ya nemi tuba.

"Ku saka wannan a kanku ku daina damunmu da wani shirmen bidiyon ku na banza".

KU KARANTA: Takardun bogi: Kotu ta hana dan takarar APC fitowa zaben maye gurbi na sanatoci

A wani labari na daban, rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaji 'yan bindiga 5, sun samu nasarar ceton mata 3 da yaransu a kauyen Diskuru da ke karamar hukumar Faskari da ke jihar Katsina, Daily Nigerian ta ruwaito.

Manjo janar John Enenche, kakakin rundunar soji, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake bayar da jawabi a kan yadda sojojin arewa maso yamma da sauran wurare a Najeriya suke tafiyar da ayyukansu tsakanin ranar 31 ga watan Oktoba zuwa 4 ga watan Nuwamba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng