Ahmad Bamalli: Kotu ta saka ranar sanar da makomar sabon sarkin Zazzau

Ahmad Bamalli: Kotu ta saka ranar sanar da makomar sabon sarkin Zazzau

- Wata babbar kotun da ke zama a Dogarawa, jihar Kaduna ta yanke ranar 5 ga wata domin yanke hukuncin sharia'r da ake yi a kan nadin sabon sarki

- Amma lauyan wanda ake kara ya ce suna fatan a fara sauraron sukar su ta karfin ikon kotun na sauraron shari'ar

- Lauyan masarautar Zazzau kuwa cewa yayi zai so mai kara da wanda ake karar su yi sasancin cikin gida domin wannan matsalar cikin gida ce

Babbar kotun jihar Kaduna da ke zama a Dogarawa, Sabon Gari a jiya ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 5 ga watan Nuwamban 2020 domin yanke hukunci a kan bukatar dakatar da sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Bamalli daga bayyana kansa a matsayin Sarkin Zazzau.

Amma kuma, lauyan sabon sarkin, Mahmoud Abubakar Magaji (SAN), ya kalubalanci ikon kotun na sauraron shari'ar, Daily Trust ta wallafa.

Magaji ya ce tunda akwai kalubale a kan iko, ana tsammanin kotun ba za ta dauka wani mataki ba har sai an warware wannan matsalar.

Ya kara da cewa, "Wasu mutane sun tunkari kotun inda suke kalubalantar nadin sabon sarkin. Mun duba takardu sannan mun mika gaban kotun.

"Mun gane cewa suna da rauni a dalilan da suka gabatar. Mun cike takardu inda muke kalubalantar ikon kotun na sauraron karar.

"Muna fatan za ta fara sauraron bukatarmu farko kafin ta duba ta su domin tamu ta fara zuwa da farko. Mun ce kotun bata da ikon sauraron wannan shari'ar. Za mu dawo ranar Alhamis domin cigaba da shari'a."

Lauyan wanda ke kara, Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, Ustaz Yunus (SAN), ya ce za su jira har zuwa ranar da aka yanke domin jin hukuncin kotun.

A bangaren lauyan masarautar Zazzau, Abdul Ibrahim, ya ce wannan rikicin na cikin gida ne.

A don haka yayi kira ga dukkan bangarori da su bada damar sasanci, ya ce zaman lafiya ne kadai zai iya rike masarautar.

KU KARANTA: Uwargidan gwamnan Kebbi ta yi martani mai zafi ga matashin da ya zargesu da nada 'yan uwa kwamishinoni

Ahmad Bamalli: Kotu ta saka ranar sanar da makomar sabon sarkin Zazzau
Ahmad Bamalli: Kotu ta saka ranar sanar da makomar sabon sarkin Zazzau. Hoto daga @GovKaduna, @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ba na goyon bayan kai wa masu zanga-zanga hari - Buhari ga matasa

A wani labari na daban, dakarun sojin saman Najeriya basu dauka kiran da aka dinga musu ba domin su kawo dauki ga jama'ar kauyen Takulashi da ke gundumar Shikarkir a karamar hukumar Chibok ta jihar Borno, majiyoyi daga rundunar ta tabbatar wa The Cable.

Wurin karfe 10 na safiyar Lahadi, wasu mayakan ta'addanci sun tsinkayi kauyen inda suka dinga harbe-harbe sannan suka banka wa gidaje wuta.

Majiyoyi daga mazauna kauyen sun sanar da cewa a kalla rayuka 11 suka salwanta kafin zuwan dakarun da ke Chibok.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng