Kada ki bari ayi tonetone: Fati Slow ta yi kacakaca da Mansura Isa (bidiyo)

Kada ki bari ayi tonetone: Fati Slow ta yi kacakaca da Mansura Isa (bidiyo)

- Fati Slow-motion ta yi kacakaca da Mansura Isa, inda tace kada ta bari su yi tone-tone

- Hakan ya biyo bayan tonon silili da Mansura ta yi wa yan matan Kannywood kan Rahama Sadau, harma ta kira wasun su da yan madigo

- Yan Kannywood dai sun caa a kan Rahama bayan bayyanar hotonta da ya janyo batanci a kan Annabi

Jarumar Kannywood wacce aka fi sani da Fati Slow-motion ta mayar da martani ga Mansura Isa a kan fallasar da ta yi wa yan matan Kannywood da suka caccaki Rahama Sadau kan shigar da tayi.

Fati ta gargadi Mansura a kan ta kiyaye ta don kada ta bari su yi tone-tone, idan ba haka ba sai ta kwance mata zani a kasuwa.

KU KAARANTA KUMA: Nasara ta samu: Rundunar ƴan sanda ta yi holen manyan ƴan fashi 4 a Katsina

Kada ki bari ayi tonetone: Fati Slow ta yi kacakaca da Mansura Isa (bidiyo)
Kada ki bari ayi tonetone: Fati Slow ta yi kacakaca da Mansura Isa Hoto: fatee_slow/mansurah_isah
Asali: Instagram

Ta kuma shawarceta da ta je ta rungumi aurenta maimakon ganinta da ake yi a tsakiyar maza a koda yaushe.

KU KARANTA KUMA: Saboda gaza ɗaukar ɗawainiya: Kotu ta warware auren shekaru 7

Jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram cewa: “Budidaddiyar wasika zuwa gareki bayarabiya yar tuwo tuwo nagode Allah nake karya banida aure ai matar aure karya tafi illar akan budurwa kuma Dan ubanki ke kinsan baki da gori akaina ko ada nina bar maki miji kika aura amma wallah idan kika cigaba da Kare masu laifi zanci ubanki na nuna maki ni mara kunyar CE ta gaske ai bansan kinyi ba sai yanxu nagani kinabata suna mace mai daraja akannywood wadda tafiki nàsaba da tarihi mai kyau arayuwa kowa yasani @hafsatshehu48 @rashidamaisaa ita uwarkice taci uwarki arashin kunya da sanin manya ita tanada bakin da zata kare kanta shrgiya yar dakan kuka yar maula yar ci da addini kina cinye kudin miskinan kiji tsoran allah ki kulada da matsalar gabanki.”

A baya mun ji cewa, tun bayan bayyanar hotunan Rahama Sadau, wadanda suka kawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani, mutane da dama musamman 'yan fim suka yi ta yin bidiyo suna la'antarta, har da masu hawayen takaici da bakinciki.

Kwatsam sai ga jaruma Mansura Isah ta yi wata wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram,mai cike da tonon silili, wacce ta harzukar da wasu daga jaruman fim din.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel