Saboda gaza ɗaukar ɗawainiya: Kotu ta warware auren shekaru 7

Saboda gaza ɗaukar ɗawainiya: Kotu ta warware auren shekaru 7

- Kotun gargajiya a Ibadan warware auren wasu masoya biyu na tsawon shekaru 7

- An raba auren ne saboda gazawar maigidan wajen ɗaukar ɗawainiyar matarsa

- Uwargidar ce ta shigar da kara inda kotun ta aiwatar da bukatarta bayan samun amincewar mijin

Wata kotun gargajiya da ke Ibadan a ranar Juma’a, ta rushe auren shekaru bakwai tsakanin Abiola Giwa da mijinta Adebimbe kan dalili na rashin kula.

A karar da ta shigar, Giwa wacce ke da haihuwa daya, ta roki kotu da ta raba aurensu saboda ta ce mijinta ya yi watsi da ita tsawon shekaru hudu.

Da yake zartar da hukunci, Cif Ademola Odunadee, Shugaban kotun ya rushe auren domin wanzar da zaman lafiya, jaridar The Nation ta ruwaito.

Odunade ya riki cewa kotun bata da wani zabi da ya wucce rushe auren tunda Adebimpe ya amince da batun raba auren da matarsa ta nema.

Saboda gaza ɗaukar ɗawainiya: Kotu ta warware auren shekaru 7
Saboda gaza ɗaukar ɗawainiya: Kotu ta warware auren shekaru 7 Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Bayan caa a kan Rahama Sadau, Mansurah Isah ta yi wa matan Kannywood fallasa

Ya mika wa Giwa ragamar kula da da guda da suka haifa sannan ya umurci Adebimpe da ya dunga biyan kudin abinin yaron 5,000 duk wata.

Da farko, Giwa ta ce: “Bayan na auri Adebimpe shekaru bakwai da suka gabata, ya kaini wani gida da babu mutane sannan ya watsar da ni a wajen.

“Ya aika mani da sakon magana cewa na bar gidan sannan na koma zama da yan uwana saboda ina da ciki.

“Ban ji daga gare shi ba bayan shekaru hudu. Ni na kula da dan da muka haifa ba tare da tallafi daga gare shi ba.

“Ban san kwanciyar hankali ba tsawon shekaru bakwai da suka gabata,” in ji ta.

KU KARANTA KUMA: Dubunnan mutane sun yi zanga-zanga kan batancin da aka yiwa manzon Allah (SAW) a Senegal

Da yake martani Adebimpe ya yarda da karar sannan ya karyata dukkanin zargin da take masa.

“Ina aikawa Abiola kudi akai-akai sannan ina mata aike. Kawai dai b azan iya daukar nauyin tsadaddiyar rayuwarta bane,” in ji Adebimpe.

A wani labarin, wata matar aure mai suna Munirat Obaro, ta roki wata kotu da ke zama a Gwagwalada ta raba aurenta na shekara 17 da mijinta, Abdullaziz Mohammed, wanda ta ke zarginsa da shaye-shaye.

Munirat, mai yara 4, wacce take zaune a Anguwar Shani, ta zargi mijinta da dukanta akai-akai har da yunkurin kasheta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng