Rashin 'yan sanda: 'Yan fashi sun samu masauki a kan babban titin Benin zuwa Auchi
- Rashin jami'an tsaro musamman 'yan sanda a Najeriya ya kawo tashin hankali a Najeriya
- Yanzu haka, 'yan fashi da masu garkuwa da mutane suna ta cin karensu babu babbaka
- Yanzu haka shugabannin IDPF sun fito fili sun roki jami'an tsaro da su dawo bakin ayyukansu
Rashin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro yasa mutane sun shiga tsaka mai wuya a titunan Najeriya, inda 'yan ta'adda suka samu dama suna cin karensu babu babbaka.
Jaridar Daily Trust ta wallafa yadda 'yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane suka fara yadda suka ga dama a titunan Najeriya, tunda suka gano cewa jami'an tsaro basa aiki, musamman 'yan sanda.
Daily Trust ta bayyana yadda jami'an tsaro suka saki ayyukansu bayan zanga-zangar EndSARS da ta barke a kasar nan.
Wannan ya biyo bayan samun damar 'yan ta'adda da bata-gari, inda suka yi ta lalata gine-gine da yin sace-sace ga gwamnati da 'yan kasuwa.
Babu jimawa Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya sanar da mutuwar 'yan sanda 22 a kasar nan sakamakon barkewar rikicin zanga-zangar EndSARS a kasar nan.
Jiya IDFP ta sanar da tabarbarewar harkokin tsaro a Najeriya saboda rashin 'yan sanda.
Shugabannin IDPF, Alhaji Ishaq Kunle Sanni da Bishop Sunday Onuoha suka sanar da hakan ga manema labarai a Abuja, inda suka bukaci 'yan sanda da sauran jami'an tsaro da su koma bakin ayyukansu don samar da zaman lafiya a kasa.
KU KARANTA: Dalilin da yasa gidajen gyaran hali basu karbar sabbin masu laifi - Ministan cikin gida
KU KARANTA: 2023: INEC ta fitar da N1bn, ta sanar da ranar cigaba da yi wa masu zabe rijista
A wani labari na daban, wata sanarwa ta fita, wacce take kunshe da ranar da za a yi bikin nadin sarautar sabon sarki, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.
A ranar Litinin ne shugaban kwamitin shirye-shiryen nadin sarautar Zazzau suka sanar da ranar Litinin, 19 ga watan Nuwamban 2020 ya zama ranar da za a yi nadin.
Za a yi nadin ne a filin wasan Polo da ke GRA, karkashin unguwar sabon gari a birnin Zaria.
An sanar da Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai zai zama babban bako a wajen nadin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng