‘Yan Sanda sun fatattaki masu zanga-zangar lumana, sun gurfanar da su a kotu

‘Yan Sanda sun fatattaki masu zanga-zangar lumana, sun gurfanar da su a kotu

- An kama wasu da su ka yi zanga-zangar #EndSARS daga Majalisa a Abuja

- Jami’an tsaro sun tattara wasu masu zanga-zangar sun kai su gaban kotu

- ‘Yan Sanda sun yi sa’a kotu ta tsare ‘yan zanga-zangar a kurkuku har 2021

A ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamba, 2020, dakarun ‘yan sanda na babban birnin tarayya su ka fatattaki wasu masu zanga-zangar #EndSARS a Abuja.

Wasu matasa sun zagaye majalisar tarayya, su na zanga-zanga domin tursasa gwamnatin Najeriya ta yi wa harkar tsaron cikin-gida garambawul.

A karshe jami’an tsaro sun fatattaki matasan da ke zanga-zangar, su ka watsa masu barkonon tsohuwa.

KU KARANTA: Za a cigaba da yajin-aiki har sai Gwamnati ta saurare mu – ASUU

Shahararren ‘dan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore, shi ne ya jagoranci masu wannan zanga-zangar, inda su ka yi wa ‘yan sandan taurin-kai.

Da ya ke bada labarin abin da ya faru, Omoyele Sowore ya ce sun kammala shirye-shiryen zanga-zangar lumuna, sai ‘yan sanda su ka kai masu hari.

Ya ce: “Mu na shirin barin wuri, sai aka kawo mana karin dakaru da su ka fara kai mana hari.”

Da ya ke bada labarin abin da ya faru, Omoyele Sowore ya ce sun kammala shirye-shiyen zanga-zangar lumuna, sai ‘yan sanda su ka kai masu hari.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi barna a gidan Kakakin Majalisar Adamawa

‘Yan Sanda sun fatattaki masu zanga-zangar lumana, sun gurfanar da su a kotu
Masu zanga-zangar EndSARS Hoto: Legit.ng
Asali: Original

“Mu na shirin barin wuri, sai aka kawo mana karin dakaru da su ka fara kai mana hari.” Inji sa.

Wata majiyar ta ce: “Yan sanda sun tsare mutane maza biyar da mace daya. Daga nan su ka yi maza su ka gurfanar da su a kotun majistare na Wuse.”

Alkalin da ya saurari shai’ar ya yanke hukuncin a tsare su a gidan kurkuku har zuwa Junairun 2021.

A makon jiya kun ji cewa Gwamnatin Tarayya za ta saida wurin samar da wutar lantarkin Afam. Gwamnati za ta samu N105bn a hannun kamfanin Transcorp.

An kammala cinikin saida wani wurin samar da wutar lantarkin ne a fadar shugaban Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel