Yunkurin kara wa’adin kwamitin Gwamna Mai Bala Buni zai jawo sabani a APC

Yunkurin kara wa’adin kwamitin Gwamna Mai Bala Buni zai jawo sabani a APC

- Kungiya ta ce za ta kai kwamitin rikon kwarya idan su ka zarce a kan mulki

- CMF ta bukaci a daina rajistar ‘yan jam’iyya, ayi zaben sababbin shugabanni

- Shugabannin jam’iyya sun yi alwashin dinke rikicin cikin gidan kafin ayi zabe

Kungiyar CMF ta yi barazanar kai karar kwamitin rikon-kwaryar jam’iyyar APC a kotu. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto.

CMF za ta shiga kotu da kwamitin Mai Bala Buni idan har ba su gudanar da zaben shugabannin jam’iyya zuwa karshen shekarar nan ba.

Haka zalika kungiyar ta nuna za ta garzaya gaban kotu muddin aka kara wa’adin kwamitin rikon.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna Dickson da Gwamna Diri sun hadu a Bayelsa

Jaridar ta ce kungiyar CMF ta ce za ta kai karar kwamitin a kotu idan ba a dakatar da rajistar da ake shirin yi wa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC.

Wannan kungiya ta ce shirin yi wa ‘yan jam’iyya rajista kokari ne na kara wa’adin kwamitin rikon ta bayan fage bayan korar Adams Oshiomhole.

Da ya ke magana da ‘yan jarida a ranar Juma’a, shugaban Concerned APC Forum, Ogenyi Okpokwu, ya ce kwamitin ya fara shirin zabe.

Tsohon ‘dan takarar gwamnan ya yi kira ga kwamitin rikon kwaryan su raba katin zama ‘dan jam’iyya ga wadanda su ka yi rajista a mazabu.

KU KARANTA: Za a cigaba da yajin-aiki har sai Gwamnati ta saurare mu – ASUU

Yunkurin kara wa’adin kwamitin Gwamna Mai Bala Buni zai jawo sabani a APC
Taron APC Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ogenyi Okpokwu ya ke cewa Mai Mala Buni da ‘yan kwamitinta su bar wa shugabannin da za a nada alhakin tattara sunayen ‘ya ‘yan jam’iyya.

Sakataren yada labarai na APC na kasa, Yekini Nabena ya bayyana cewa za su hada-kan ‘ya ‘yan jam’iyya kafin a shirya zaben shugabanni na kasa.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana game da fastocinsa na takarar shugabancin kasa da su ka fara yawo a bangarorin kasar nan.

Malam Nasir El-Rufai, ya musanta sanin wanda ya ke da alhakin hada hotunansa a fostoci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng