Za a saida Afam a kan kudi Naira Biliyan 105 inji Shugaban hukumar BPE

Za a saida Afam a kan kudi Naira Biliyan 105 inji Shugaban hukumar BPE

- Ana sa ran yau a kammala cinikin saida Afam Power Plant a Aso Villa

- Gwamnatin Tarayya za ta saida wa ‘yan kasuwa wurin samar da wutan

- Za a saida wa Transcorp PLC tashar lantarkin ne a kan Naira biliyan 105

Gwamnatin tarayya za ta samu Naira biliyan 105 daga saida wurin samar da wuta na Afam. Vanguard ta fitar da wannan rahoto a yau da safe.

Shugaban hukumar BPE mai alhakins saida kadarorin gwamnatin tarayya, Alex Okoh, ya shaida wa ‘yan jarida wannan a ranar 4 ga watan Nuwamba.

Alex Okoh ya ce za a karkare cinikin nan ne a fadar shugaban kasa na Aso Villa a birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Minista ta na goyon bayan a shigo da Matasa a cikin Gwamnati

A cewar Mista Alex Okoh, duk da annobar COVID-19 da ta jagwula lissafi, hukumar BPE ta cigaba da gudanar da ayyukanta ba tare da gaza wa ba.

Okoh ya kuma karyata rahotonnnin da ke yawo cewa hukumar BPE ta yi awon gaba da wasu Naira biliyan 2.5 daga cikin kudin da aka saida PHCN.

BPE ta yi karin haske game da gaskiyar yadda lamarin ya ke:

“A ranar 25 ga watan Fubrairun 2014, BPE ta samu dama daga OAGF na samun alaka da kamfanin Aso Savings & Loans Plc., su ka adana N2.5bn a asusunsu.”

KU KARANTA: Yadda Fasto ya jawo kashe Musulmai da asarar dukiya mai yawa – NSCIA

Za a saida Afam a kan kudi Naira Biliyan 105 inji Shugaban hukumar BPE
Ministan wuta Saleh Mamman Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Shugaban BPE ya ce an yi wannan ne 2014 domin gina gidajen ma’aikata, amma a karshe ma’aikatan ba ta ba su samu damar cin moriyar tsarin ba.

Okoh ya ce a 2015 aka bada umarnin dauke duk wasu kudi a maida su asusun bai-daya na TSA a CBN, wannan ya sa aka fara shirin dawo wa BPE kudinta.

Dazu kun ji cewa Mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya ci karfin aikin matatar danyen mai da ake yi, sannan za a bude katafaren kamfanin takin na Dangote.

A duk rana ta Allah, matatar Dangote za ta tace gangar danyen mai 650, 000 idan ta fara aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel