Babban dalilin da yasa aka tsige Rashidi Ladoja daga gwamna a shekarar 2006 - Obasanjo
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi waiwaye adon tafiya a kan dalilin tsige tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja
- Ladoja ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Oyo a shekarar 2003 amma sai aka tsige shi kafin ya kammal wa'adinsa na farko
- An samu mabanbantan rahotanni a kan dalilin tsige Ladoja a wancan lokacin
Tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana babban dalilin da yasa aka tsige tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja.
Obasanjo ya bayyana hakan ne lokacin taron gabatar da littafin tarihin Adebayo Alao-Akala, wani tsohon gwamnan jihar Oyo.
A cewar Obasanjo, an tsige Ladoja ne sakamakon rashin ɗa'a ga Marigayi Lamiidi Adedibu, ubangidan siyasar jihar Oyo, da kuma Yekinni Adeoja (mashahurin ɗan siyasa a jihar).
Obasanjo wanda yace ya gano cewa Ladoja ya fara rigima da shi a littafin tarihin Alao-Akala inda yace Ladoja ya biya maƙudan kuɗaɗe don a ɓoye aibunsa.
DUBA WANNAN: A karshe: Obasanjo ya fadi abinda ya rusa takarar Atiku lokacin da yaso bijire masa a 2003
"Ka rubuta a shafi na 140 cewar Ladoja ya fara rigima da ni sakamakon rashin bani goyon baya domin yin tazarce a karo na uku, wanda babu shi a tsarin doka," a cewarsa.
"Ban san cewa Ladoja yana rigima dani ba, kuma dalilin zamansa gwamna albarkacin gudunmawar da ya samu ne daga mutane biyu; wato Lamidi Adedibu da Yekenni Adeojo.
"Na roƙe shi akan ya basu matsuguni gaba ɗayansu, amma sai yace min dukkansu mutanen Ibadan ne don haka su san inda zasu sa kansu.
DUBA WANNAN: Karya kake, ba'a sulhunta rikicin APC a Zamfara ba - Marafa ya bukaci Buni ya yi murabus
"Ta tabbata cewa ya yi dai-dai domin kuwa sun san inda suka yi da kan nasu. Sai dai kuma sakamakon haka al'amura sun kwaɓewa Ladoja, don kuwa ya kwana ciki."
A lokacin, Alao-Akala shine mataimakin gwamnan jihar Oyo, daga shekarar 2003-2007, kafin daga bisani ya maye gurbin Ladoja bayan an tsige shi daga kujerar gwamna.
A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, rundunar sojin saman Nigeria (NAF) ta ce zata tura da jiragen sama marasa matuki zuwa Zamfara don bunkasa aikinta na yaki da 'yan bindiga a jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng