Obasanjo ya fadi abinda ya rusa takarar Atiku lokacin da yaso bijire masa a 2003

Obasanjo ya fadi abinda ya rusa takarar Atiku lokacin da yaso bijire masa a 2003

- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi tsokaci a kanyadda abotar Atiku da Ekwueme ta ruguje a shekarar 2003

- A cewar Obasanjo, Atiku bai jan daga takarar kujerar shugaban kasa ba a shekarar 2003

- Rahotanni sun sha kawo gulmar cewa da kyar Obasanjo ya lallashi Atiku domin ya hakura da takarar shugaban kasa, su kammala mulki, zai bashi takara tunda arewa za ta koma

Tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce amintakar tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar, da Dakta Alex Ekwueme lokacin zaɓen cikin gida na jam'iyyar PDP a shekarar 2003 ta rushe bayan Ekwueme ya sha kaye a zaɓen.

Obasanjo ya faɗi hakan ne lokacin taron gabatar da littafin 'Amazing Grace,' tarihin tsohon gwamnan jihar Oyo, Chief Adebayo Alao-Akala.

Obasanjo, wanda ya kasance Shugaban taron gabatar da littafin, ya yi bayanin abinda da ya wakana a zahiri bayan marubucin ya yi da'awar Atiku ne ya nemi tafiyar ta rushe kafin zaɓen cikin gida.

KARANTA: Karya kake, ba'a sulhunta rikicin APC a Zamfara ba - Marafa ya bukaci Buni ya yi murabus

Obasanjo yace; "kuma Atiku bai juyawa tafiyar baya ba har sai bayan da Alex Ekwueme ya sha kaye a zaɓen cikin gida.

"Kamar yadda suka tsara, suka kuma yarda akai, Atiku zai kasance mataimakin Ekwueme, shi kuma Ekwueme a matsayin Shugaba, a nufinsu idan Atiku ya shafe shekaru uku a matsayin mataimaki sai ya ajiye aikin ya tsaya takara da ƙafarsa a shekarar 2007.

Obasanjo ya fadi abinda ya rusa takarar Atiku lokacin da yaso bijire masa a 2003
Obasanjo @Punch
Asali: UGC

"Sai bayan kammala zaɓen cikin gida ne Atiku ya juya baya,wato bayan yaga babu sarki sai Allah, ba wata sauran mafita."

KARANTA: Ku dakatar da Buhari daga fita waje domin duba lafiya - Majalisa ta gargadi fadar shugaban kasa

Obasanjo ya ɗora laifin gazawar kudu maso yamma a wajen fidda shugaban majalisar wakilai sakamakon irin rawar da Alao-Akala ya taka, wacce har daga ƙarshe Aminu Waziri Tambuwal ya lashe kujerar.

Ya ce da farko Alao-Akala ya ce ya goyi bayan Ajibola Muraina, kuma da mu da shi duk mun amince da hakan, amma sai daga baya ya sauya ra'ayinsa zuwa Mulikat Akande, wacce a karshe ta sha kaye a hannun Tambuwal.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng