Karya kake, ba'a sulhunta rikicin APC a Zamfara ba - Marafa ya bukaci Buni ya yi murabus

Karya kake, ba'a sulhunta rikicin APC a Zamfara ba - Marafa ya bukaci Buni ya yi murabus

- Tsohon sanata Kabiru Marafa ya ce shugaban riko na jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, ya sharara karya

- Sanata Marafa ya bukaci Buni da sauran mambobin kwamitinsa na rikon kwarya da sulhu su yi murabus ko a saukesu daga matsayinsu

- A cewar tsohon dan majalisar, har yanzu hedikwatar APC biyu ce a Zamfara kuma basa ga maciji da juna

Kabiru Marafa, tsohon daga Zamfara ta tsakiya, ya zargi gwamna Mai Mala Buni, mai kula da kwamitin sulhun jam'iyyar APC, da shararo zuƙi ta malle.

A cewar Marafa, batun sulhunta rikicin jam'iyyar a jihar Zamfara duk shifcin gizo ne, ba gaskiya bane kamar, yadda kwamitin ke da'awar ya sulhunta komai.

Marafa yace Buni, gwamnan jihar Yobe, ya saɓa lamba kuma ba gaskiya yake faɗa game da rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar APC a Zamfara ba, don ko kusa ba'a sulhunta komai ba game da dambarwar siyasa da jam'iyyar da fada ba.

Haka zalika, ya gargaɗi gwamna Mai Mala Buni mai kula da kwamitin da kada ya rusa jam'iyyar APC, idan kuma ba zai iya jagorancin ba ya yi murabus kawai.

KARANTA: Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa

Kwamitin a taron ƙarshen da ta gudanar ranar Talata sun yi iƙirarin cewa sun sulhunta rikicin a jam'iyyar a jihohin Bauchi, Cross River, Edo, Ekiti, Enugu, Zamfara, Ondo, da kuma Oyo.

Karya kake, ba'a sulhunta rikicin APC a Zamfara ba - Marafa ya bukaci Buni ya yi murabus
Buni da Marafa
Asali: UGC

Marafa ya bayyana cewa har yanzu hedikwata biyu APC ke da ita a jihar Zamfara, a birnin Gusau, wanda basa ga maciji da juna.

Ƙananan hukumomi 14 sun ce"Wannan iƙirarin na kwamitin zai ƙara ta'azzara rikicin jam'iyyar a jihar Zamfara", a cewarsa.

KARANTA: Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi martani da sagube a kan tsine mata a Masallatai

Marafa yace, "wannan kalaman sun gurgunta gaskiyar jam'iyyar da kwarjininta, ta hanyar kautar da hankalin jama'a.

''Kwamitin ya rasa aminci da kima a idon jama'a. Ya zama dole ƴan kwamitin su ajiye muƙamansu ko kuma a saukesu daga matsayinsu.

''Kwamitin ya gaza tab'uka wani abin azo a gani tun kafuwarshi.

''Wannan maganar karya ce tsagwaronta. Ina addu'ar Allah ya sa ba ruguza jam'iyyar za su yi ba.

''Ba wani wanda suka tuntuba a Zamfara don haka batun su ce sunyi sulhu bai taso ba kwata kwata.''

A ranar Alhamis ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa majalisar dattijai ta gargadi ma'aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) su dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel