Iyan Zazzau Bashir Aminu ya maka El-rufai a kotu saboda nada Bamalli sarki
- Daya daga cikin wadanda suka nemi saurautar Zazzau, Iyan Zazzau Aminu Bashir ya yi karar gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai a kotu kan nada Ahmed Nuhu Bamalli sarki
- Aminu Bashir na neman kotun ta bada umurnin tsige Nuhu Bamalli sannan ta bada umurnin a nada shi sabon sarkin Zazzau
- Acewar karar da Aminu Bashir ya shigar, shine ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben da masu zaben sarki suka yi tunda farko don haka shi ya dace ya zama sarki
Iyan Zazzau, Bashir Aminu, ya yi karar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a kotu saboda nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau don maye gurbin Dakta Shehu Idris da ya rasu a ranar 20 ga watan Satumba.
A cikin karar da ya shigar a babban kotun jihar Kaduna a ranar Litinin, Aminu na son kotun ta bada umurnin nada shi sarki duba da cewa shine ya fi samun kuri'u mafi yawa a zaben da masu zaben sarki suka yi kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
Idan ba a manta ba a ranar 25 ga watan Satumba, masu zaben sarki na masarautar Zazzau karkashin jagorancin Wazirin Zazzau, Ibrahim Aminu ya mika jerin sunayen yarimomi uku don zaben daya daga cikinsu a matsayin sabon sarki.
DUBA WANNAN: Ganduje ya dakatar da hadiminsa Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Buhari
Wadanda aka mika sunayensu sune Bashir Aminu, Iyan Zazzau da ya samu kuri'u 89; Munir Jafaru, Yariman Zazzau ya samu kuri'u 87; Aminu Shehu Idris, Turakin Karamin Zazzau ya samu kuri'u 53.
Amma a ranar 1 ga watan Oktoban 2020, gwamnan jihar Kaduna ya soke sunayen wadanda masu zaben sarkin suka mika masa.
A cewarsa, masu zaben sarkin ba su yi adalci ba ga sauran masu neman sarautar kuma ya bukaci a bawa sauran masu neman sarautar shiga takarar.
Sakataren gwamnatin jihar, Balarabe Lawal ya yi bayanin cewa gwamnati ta bada umurnin yin sabon zabe bayan soke na farko saboda an cire sunayen mutum biyu daga cikin masu neman sarautar.
KU KARANTA: Labari da dumi-dumi: IGP ya soke rundunar SARS a Najeriya
Daga bisani gwamnan ya nada Mista Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarki ya yi watsi da zaben na farko da masu zaben Sarkin Zazzau suka yi.
A kofin takardar karar da majiyar Legit.ng ta gani, mai shigar da karar ya maka mutum 10 a kotu da suka hada da Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Attoney Janar na jihar Kaduna; Majalisar Sarakunan Kaduna; Majalisar Masarautar Zazzau; Wazirin Zazzau, Ibrahim Aminu; Fagacin Zazzau, Umaru Muhammad; Makama Karamin Zazzau, Mohammed Abbas; Limamin Juma'an Zazzau, Dalhatu Kasimu Imam; Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli.
A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dakta Yusuf Jibrin a matsayin shugaban asibitin koyarwa na Jamiar Tafawa Balewa, ATBUTH da ke Jihar Bauchi.
Ministan Lafiya, Dakta Osagie Ehanire ne ya tabbatar da hakan a ranar Jumaa a Abuja inda ya ce nadin da aka masa na shekaru hudu ne kuma zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Satumban 2020.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng