Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli

Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli

- A ranar Laraba 7 ga watan Oktoba ne aka nada Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli matsayin sarkin Zazzau

- Nadin na zuwa ne sakamakon gurbin da aka samu a masarautar bayan rasuwar tsohon sarki Alh Shehu Idris da ya rasu a ranar 20 ga watan Satumba

- Kafin nadi shi sarki, Ahmad Nuhu Bamalli ya rike mukamai da dama na baya-bayansu shine jadakar Najeriya a kasar Thailand

Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, sarkin Zazzau na 19 shine tsohon jakadar Najeriya a kasar Thailand.

A ranar Laraba 7 ga watan Oktoban ne Gwamna Nasiru El Rufai ya sanar da nadinsa a matsayin sabon sarkin Zazzau.

Ga wasu hotunan sabon sarkin a lokacin da ya ke jakadar Najeriya a kasar Thailand a 2017.

Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli
Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli (Magajin Garin Zazzau na wancan lokacin) ta Sarkin Thailand, Mai Martaba Maha Vajiralongkorn a fadarsa da ke Bangkok.

Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli
Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli a lokacin da ya kai wa Farai Ministan Thailand, Gen Prayut ziyara.

DUBA WANNAN: Yariman Zazzau, Munir Ja'afaru ya taya Ahmed Bamalli murnar zama sabon Sarkin Zazzau

Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli
Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Jakadan Najeriya a Thailand, a lokacin da ya shirya wa tsohon gwamnan Kano, Muhammadu Sanusi II liyafa a Bangkok Thailand a lokacin da tsohon sarkin ya ziyarce shi.

Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli
Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli
Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli tare da matarsa a lokacin da suka kai wa Sarkin Thailand ziyara a fadarsa.

KU KARANTA: Hatsarin mota ta yi sanadin rasa rayyuka 9 a Kano

Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli
Hotuna: Ku sadu da sabon Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Sabon sarkin Zazzau, Ambassada Ahmad Nuhu Bamalli lokacin da ya dawo Najeriya a filin tashin jirage na Nnamdi Azikiwe a Abuja ranar 23 ga watan Satumba bayan rasuwar marigayi Sarkin Zazzau Alh Shehu Idris a ranar 20 ga watan Satumba.

A wani labarin daban, Gwamnatin tarayya ta bada umurnin masu amfana da shirin N-Power na Batch A da B da ba su samu kudadensu na watanni baya ba su tafi ofisoshin wakilansu na jihohi domin sake tantance su.

Ministan jin kai da kare afkuwar balai, Sadiya Umar Faruk ce ta bada wannan umurnin a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164