Bashin $1.2bn: Kar ka mayar da Nigeria ƙasar mabarata - PDP ta gargaɗi Buhari
- Jam'iyyar PDP ta caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan shirin ciyo bashi da yake yi daga kasar Brazil
- PDP ta gargadi Buhari a kan cewa kar ya mayar da Najeriya ƙasar mabarata da tarin bashin da yake karbowa
- Ta ce ya kamata majalisar tarayya ta taka masa birki
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa a kasar, ta yi wa gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo a kan shirin karbo bashi da take yi daga kasar Brazil.
PDP ta koka a kan halin da kasar za ta shiga idan har Shugaba Buhari ya ci gaba da ciyo irin wannan tarin bashi, inda tace zai gurgunta kasar ne.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar dauke da sa hannun kakakinta, Kola Ologbondiyan.
KU KARANTA KUMA: Karshen alewa kasa: An kama makasan dan majalisar jihar Bauchi
Ta ce: “Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jan hankali kan sabon bashin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin ciyowa na $1.2biliyan daga kasar Brazil, duk da kokawar da jama’a ke yi a kan yawan bashin da aka karbo daga China da sauran kasashen waje.
“PDP na gargadin fadar shugaba Buhari da kada ta ci gaba da kassara kasarmu da kuma amfani da shirin noma a matsayin tsanin ci gaba da karbo bashi daga waje, ba tare da duba kalubalen da talakawa da wadanda za a haifa nan gaba za su fuskanta ba.
“Ya kamata majalisa ta taka wa Buhari burki wajen kara ciyo bashi, saboda zai jefa kasar nan cikin mawuyacin hali, ya kuma nakasa harkar noma da bunkasa tattalin arzikin abincinmu.
“Muna jan hankalin ’yan Najeriya da cewa in har aka karbo bashin Naira biliyan 459 daga Brazil, baya ga Naira Tiriliyan 5.20 da ke cikin kasafin 2021, bashin da aka ciyo wa kasar nan zai doshi Tiriliyan 36.2 kuma zai iya jefa tattalin arzikinmu cikin mummunan hali.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun saki alkalan Zamfara da suka yi garkuwa da su bayan an biya kudin fansa
“PDP tana kiran majalisa da ta yi wa tsarin karbo bashi gyaran fuska domin kare kasar nan daga fadawa mawuyacin hali.
“Maimakon tulin bashin da gwamnati Buhari ke ciwowa, gara ta mayar da hankali wajen kirkiro hanyoyin samun kudade a cikin gida.”
A wani labarin, majalisar dattijai ta gargadi ma'aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) su dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa.
A cewar majalisar, yin hakan zai tabbatar da cewa asibitin fadar shugaban kasa ya koma hayyacinsa a cikin shekarar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng