Yanzu-yanzu: Bayan fadi a Wisconsin, Trump ya bukaci kotu ta dakatad da kirgan kuri'u a Michigan

Yanzu-yanzu: Bayan fadi a Wisconsin, Trump ya bukaci kotu ta dakatad da kirgan kuri'u a Michigan

- Kamar yadda yayi alkawarin, Trump ya shigar da bukata kotu

- Da farko a dakatad a kirgan kuri'u a Michigan, sannan a sake kirga kuri'un Wisconsin

Trump na kan shan kaye hannun abokin hamayyarsa, Joe Biden

Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar Laraba ya shigar da kara kotu inda ya bukaci a dakatad da kirga kuri'u a jihar Michigan, inda abokin hamayyarsa, Joe Biden, ke kan gaba.

Diraktan yakin neman zaben Trump, Bill Stepien, ya yi zargi duk da cewa bai gabatar da hujja ba cewa ba'a baiwa mambobinsu daman lura da yadda ake kirgan kuri'u a wurare da dama ba.

Hakazalika, kwamitin yakin neman zaben Trump ya bukaci sake kirgan kuri'un Wisconsin bayan shan kaye da tazara karami.

"Akwai rahotannin magudi a wurare daban-daban a Wisconsin kuma hakan ya cusa mana shakkun sakamakon," Diraktan Kamfen Trump, Bill Stepien ya bayyana.

"Shugaban kasan na da daman bukatan sake kirgan kuri'un kuma zamu yi ba tare da bata lokaci ba."

Biden ya lashe zaben Wisconsin da kuri'u 20,000.

Yanzu jihohin da ake sauraron sakamakonsu sune Georgia, North Carolina, Nevada, Michigan, da Pennsylvania.

KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 214, Biden 248

Yanzu-yanzu: Bayan fadi a Wisconsin, Trump ya shiga bukaci kotu ta dakatad da kirgan kuri'u a Michigan
Yanzu-yanzu: Bayan fadi a Wisconsin, Trump ya shiga bukaci kotu ta dakatad da kirgan kuri'u a Michigan
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Shugaba Trump ya na banbami, ya ce wasu sun yi zabe bayan lokaci ya kure

Mun kawo muku cewa Trump ya yi kuka, ya ce ana yi masa magudi.

A jawaban da ya saki a shafinsa na Tuwita, ya ce ana kokarin shafe masa kuri'un da ya samu a Pennsylvannia.

"Suna iyakan kokarinsu wajen kwashe kuri'u na 500,000 da nike da shi a Pennsylvania. Hakazalika Michigan da sauransu," Trump yace.

"Kawai kuri'un Biden ake gani a ko ina, Pennsylvania, Wisconson da Michigan. Gaskiya haka bai da kyau ga kasar mu,"

"Wai shin meyasa duk lokacin da aka kirga kuri'un akwatin sako lalata min abubuwa sukeyi," Trump ya kara

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel