Wadanda ake zargi da laifin yi wa Sanata Oriolowo fashi sun shiga hannu

Wadanda ake zargi da laifin yi wa Sanata Oriolowo fashi sun shiga hannu

- ‘Yan Sanda sun kama wasu da zargin yi wa Adelere Adeyemi Oriolowo fashi

- Shi Adelere Adeyemi Oriolowo, Sanata ne mai wakiltar jihar Osun a majalisa

- Wadanda ake tuhuma sun musanya zargin, Alkali ya tsare su a gidan kurkuku

A ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba, 2020, kotun majistare da ke Osogbo a jihar Osun ta tsare wasu mutum uku da ake zargi da laifin fashi.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto dazu cewa Alkali ya bada umarnin a rike Saheed Muslim, Kazeem Ganiyu da wani Olaleye Olawale a gidan yari.

Lauyan da ke kare ‘yan sanda, ya shaida wa kotu cewa wadanda ake tuhuma sun shiga gidan Adelere Adeyemi Oriolowom, sun yi gaba da kaya.

KU KARANTA: Uwargida ta banka wa kishiyarta wuta

Adelere Adeyemi Oriolowo Sanata ne mai wakiltar mazabar Osun ta yamma a majalisar dattawa.

ASP Idoko John ya na zargin mutanen ukun nan sun yi wannan ta’adi ne a ranar 24 ga watan Oktoba, 2020 da kimanin karfe 7:00 a garin Iwo.

Idoko Saheed Muslim, Kazeem Ganiyu da Olaleye Olawale sun rike miyagun makamai da gatari, karafuna, da sanduna yayin da su ka kutsa gidan.

Daga cikin kayan da mutanen su ka sace kamar yadda mai kare jami’an tsaro ya fada akwai manyan akwatin talabijin shida da kudinsu ya kai N2m.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun harbe wani 'dan fashi a Katsina

Wadanda ake zargi da laifin yi wa Sanata Oriolowo fashi sun shiga hannu
Kotun majistare
Asali: UGC

Ta bakin lauyan da ya tsaya masu, Taiye Tewogbade, wadanda ake tuhuma sun karyata zargin da aka jefe su da su, su ka ce ba su aikata laifuffukan ba.

Bayan ya saurari shari’ar, Alkali M. A Awodele ya bada umarni a rufe su a gidan yari, sannan ya bukaci a kai karar zuwa gaban Alkalin kotun Iwo.

A birnin tarayya, mun ji cewa Lai Mohammed ya yi gumi a gaban Sanatoci wajen kare kasafin kudin shekarar 2021, inda ake zage shi da badakala.

‘Yan Majalisa sun karyata Ministan yada labaran a kan kwangilar gina tashar NTA a jihar Yobe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel