Kumallon mata: Uwargida ta bankawa gidan kishiyarta wuta a Kano

Kumallon mata: Uwargida ta bankawa gidan kishiyarta wuta a Kano

- Wata uwargida da zafin kishi ya kwasa ta cinnawa gidan kishiyarta wuta a unguwar Gwazaye da ke Kano

- Uwargidan ta cinnawa gidan amarya wuta ne bayan mijinsu ya bata ajiyar makullin gidan amaryarsa a lokacin da zasu fita unguwa da amaryar tasa

- Jami'an 'yan sanda sun yi awon gaba da wannan uwargida da ta tafka wanna katobara domin zurfafa bincike

Ana zargi wata uwargida da cinnawa gidan kishiyarta wuta saboda tsananin kishi.

Lamarin ya afku a Unguwar Liman da ke yankin garin Gwazaye a karkashin ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano da yammacin ranar Lahadi.

Uwargidan ta aikata wannan aika-aika ne lokacin da amaryar ta fita unguwa.

Shaidun gani da ido sun tabbatarwa da Freedom Radio da ke Kano cewa sun hangi lokacin da uwargidan tayi fitar burtu daga cikin gidan a daidai lokacin da maƙwabta suka fara shelar neman ɗaukin kashe wutar da ta tashi.

KARANTA: Mijina ya na tilasta min akan lallai sai na bashi damar shan jinin al'adarta - Matar aure a gaban kotu

Mai gidan mai suna Malam Ilyasu Abdullahi Umar ya ce tabbas biri ya yi kama da mutum domin kuwa tabbas ya bar mukullin gidan amaryarsa a hannun uwargidansa lokacin da ya je kai amaryar gidansu domin ta ziyarci gida a karon farko cikin watanni uku bayan auren su.

Kumallon mata: Uwargida ta bankawa gidan kishiyarta wuta a Kano
Kumallon mata: Uwargida ta bankawa gidan kishiyarta wuta a Kano
Asali: Getty Images

Ita ma Amaryar ta tofa albarkacin bakinta akan dambaruwar inda ta ce akwai buƙatar mata su rage zafin kishi mai tsanani.

Kana ta ce wutar ta babbake kayan ɗakinta ƙurmus banda kujerarta mai biyu ta ita kaɗai tayi saura.

KARANTA: Kotu ta datse igiyar auren shekara 10 bayan mata ta zargi miji da halin bera

Dukkan koƙarin jin ta bakin uwargidan yaci tura, don kuwa ta turje, ta yi funfurus tare da yin gum da bakinta a yayin da manema labarai suka yi mata tambaya.

Tuni jami'an ƴansanda suka yi awon gaba da wannan uwargida, uwar katoɓara, domin gudanar da bincike.

A ranar 2 ga watan Nuwamba ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa Malamar mata, marubuciya, kuma fasto a Cocin Agape Ministries, Funke Adejomo, ta ce mayun mata sune silar talaucewar maza da yawa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel