‘Yan Majalisa sun dura kan Lai Mohammed saboda kwangilar N250m
- Sanatoci sun zargi Ma’aikatar yada labarai da kin yin aikin tashar NTA a Gashua
- ‘Yan Majalisar sun ce duk da an ware duk kudin aikin, babu abin da aka kammala
- Bayan haka ‘Yan Majalisar Dattawa sun yi kaca-kaca da Ministan ayyuka da gidaje
A ranar Talata jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa majalisar dattawa ta shake ministan yada labarai, Lai Mohammed a dalilin wata kwangila.
Ma’aikatar yada labarai ta cusa wata kwangila ‘ERPG 10145116’ a kasafin kudin shekarar 2020 wanda gwamnatin tarayya ta dauki nauyin aikin.
Rahoton ya bayyana cewa an ba ma’aikatar yada labarai Naira miliyan 250 domin wannan aiki.
KU KARANTA: Sabon karin farashin kudin shan wutar lantarki ya jawo babatun Jama’a
Ministan ya jagoranci sauran manyan ma’aikatarsa a ranar Talara, 3 ga watan Nuwamba, 2020, domin su kare kasafin kudin 2021 a gaban majalisa.
Shugaban kwamitin yada labarai a majalisar dattawa, Sanata Abdullahi Sankara, ya ce su na bin Lai Mohammed bashin bayani game da kwangilar.
Abdullahi Sankara ya ce duk da an biya kudin kwangilar cif, amma babu alamun an kama hanyar kammala wannan aiki na gina tashar NTA a Gashua.
An samu sabani a lokacin da Ministan ya bayyana cewa wani ‘dan majalisa ya dauki nauyin kwangilar, aka sake cusa ta a cikin kasafin kudin 2020.
KU KARANTA: Mai dakin Buhari ta yi alkawarin gina dakunan yaki da Kansa
Sanatocin da ke sauraron kwamitin sun karyata Lai Mohammed, su ka ce sam ba abokin aikinsu ya yi wannan kwangila a matsayin aikin mazabarsa ba.
A daidai wannan lokaci kuma NNPC ta lamushe N350bn a matsayin albashin shekara guda.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng