Dan Najeriya ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai a Amurka
- Dan Najeriya Oye Owolewa ya zama dan majalisa mai wakiltar Columbia a kasar Amurka bayan ya lashe zabe a karkashin jam’iyyar Democrat
- Oye dai ya sami kaso 82.65 cikin 100 wanda ya kai kuri’u 135,234 inda ya kayar da abokan hamayyarsa
- Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki ya taya shi murnar wannan nasara da yayi
Wani haifaffen dan Najeriya a karkashin jam’iyyar Democrat, Oye Owolewa, ya lashe zaben kujerar dan majalisa mai wakiltan gundumar Columbia a kasar Amurka.
Hakan na kunshe ne a cikin wani wallafa da shafin ABC 7 News tayi a safiyar ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba.
Bisa ga sakamakon zaben, Oye sami kaso 82.65 cikin 100 wanda ya kai kuri’u 135,234 inda ya kayar da abokan karawarsa Joyce Robinson-Paul wanda ya sami kuri’u 15,541, da kuma Sohaer Syed wanda ya samu kuri’u 12,846.
KU KARANTA KUMA: Karshen alewa ƙasa: Ƴan sanda sun bindige ɗan fashi a Katsina
Oye Owolewa mai shekaru 30, ya fito ne daga yankin Omu-Aran da ke jihar Kwara, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Owolewa ya kasance daya daga cikin yan Najeriya tara da ke takara a zaben Amurka.
Ya kammala karatun digirin digir-gir dinsa a fannin Kimiyyar Harhada Magunguna daga Jami’ar Norteastern da ke birnin Boston a kasar ta Amurka.
Tuni dai ’yan Najeriya da dama suka fara mika sakon fatan alheri da taya murna ga Mista Oye, ciki har da tsohon gwamnan jihar Kwara kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki.
KU KARANTA KUMA: Bidiyo: Takaicin soyayya ya sa matashin Likita fashewa da kuka a gaban marasa lafiya
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Laraba, Saraki ya ce:
"Ina taya Oye Owolewa (@AdeoyeOwolewa) murna, kan zabarsa da aka yi a matsayin dan majalisar wakilai na gudunmar Columbia. Nasararsa wata ’yar manuniya ce kan cewa matasan Najeriya za su iya cimma manyan burikansu a rayuwa."
Ihlan, 'yar shekara 38 ta doke abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican Lacy Johnson, wanda bakin fata ne kuma attajiri, da kashi 64.6% - 25.9% na kuri'u, Aljazeera ta ruwaito daga The Associated Press.
Ilhan Umar ce yar asalin kasar Somaliya ta farko da ta samu shiga majalisa kuma daya cikin mata musulmai biyu da aka fara zaba a tarihi a 2018.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng