Za a samu hauhawar wadanda zasu kamu da cutar korona a karo na biyu - FG

Za a samu hauhawar wadanda zasu kamu da cutar korona a karo na biyu - FG

- Yawan masu korona a Najeriya zai karu sosai nan da makonni biyu masu zuwa

- Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba

- Mustapha ya ci gaba da bayyana cewa zabukan gwamnan Edo da Ondo, da kuma zanga-zangar EndSARS ne za su haddasa haka

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da tsoron kwararru a harkar lafiya da dama a fadin duniya game da dawowar annobar cutar korona a karo na biyu.

Boss Mustapha, babban sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin Shugaban kasa kan COVID-19 a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba, ya bayyana cewa za a fasinjoji da yawa za su shigo da cutar cikin kasar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mustapha ya daura laifin haka a kan wasu yan Najeriya da suka ki daukar gwaje-gwajen da ya kamata a yayinda suka iso kasar, inda ya bayyana cewa daga alkaluman mahukunta, mutum daya cikin uku ne ke gabatar da kansu don gwaji.

Za a samu hauhawar wadanda zasu kamu da cutar korona a karo na biyu - FG
Za a samu hauhawar wadanda zasu kamu da cutar korona a karo na biyu - FG Hoto: @PremiumTimesng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Mu masu tsantsar biyayya ne ga shugaban kasa - Buratai

Babban sakataren gwamnatin ya kara da cewa zabukan Edo da Ondo, da kuma zanga-zangar EndSARS a fadin kasar, sun kara yawan cutar.

Ya ce:

“PTF na ta jaddada wadannan lamura saboda muna cikin hatsarin shigowa da cutar, tunda an bude hanyar jiragen samanmu da kuma yawan yaduwar cutar sakamakon zanga-zanga. Makonni biyu masu zuwa za su zamo cike da hatsari."

KU KARANTA KUMA: Muna kokarin hana sake barkewar zanga-zangar EndSARS a karo na biyu – Shugaban gwamnonin Arewa

Mustapha ya bayyana cewa PTF ta yi barazanar daukar mataki a kan masu take doka sannan ta lura cewa da dama basa bayar da hadin kai.

A gefe guda, mun ji cewa Gwamnatin jihar Legas na iya sa sabuwar dokar hana fita da ma wasu tsauraran matakai idan aka samu barkewar sababbin masu dauke da cutar COVID-19.

Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba, 2020.

Rahoton ya ce wannan sanarwa ta fito ne daga bakin darektan yada labarai na ma’aikatar lafiyar jihar Legas, Tunbosun Ogunbanwo a ranar Talata da rana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel