Mu masu tsantsar biyayya ne ga shugaban kasa - Buratai

Mu masu tsantsar biyayya ne ga shugaban kasa - Buratai

- Rundunar sojin Najeriya ta ce ba za ta janye biyayyarta da jajircewarta wajen kare damokradiyyar Najeriya ba

- Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya ce babu tantama a kan biyayyar jami’an rundunar sannan kuma cewa zai ci gaba da kasancewa a haka

- Buratai mai shekaru 59 ya bayyana hakan ne a wani taron zabar manyan jami’ai a jihar Kaduna

Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya jaddada biyayyar jami’an rundunar sojin Najeriya ga gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buratai ya bayyana matsayinsa ne yayin da yake jawabi a wajen bude taron rundunar sojin Najeriya na kwanaki biyu a Zaria, jihar Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Muna kokarin hana sake barkewar zanga-zangar EndSARS a karo na biyu – Shugaban gwamnonin Arewa

Mu masu tsantsar biyayya ne ga shugaban kasa - Buratai
Mu masu tsantsar biyayya ne ga shugaban kasa - Buratai Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Shugaban sojin ya samu wakilcin kwamandan dakarun sojin kasar, Manjo Janar Stevenson Olabanji a taron, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kalamansa:

“Zan fara da mika godiyata ga Shugaban kasa kuma babban kwamadan rundunar sojin Najeriya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan goyon bayan da yake ci gaba da ba rundunar sojin kasar wajen sauke hakkin da ya rataya a wuyanta.

“Don haka, na dauki alwashin tabbatar da jajircewa da biyayyan jami’an rundunar sojojin Najeriya ga Shugaban kasa da kuma kare martabar damokradiyyarmu.”

Shugaban sojin ya ce ya bayar da muhimmanci wajen horo da sake horar da jami’an rundunar sojin domin aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata.

A gefe guda, Sojojin Amurka na tawagar SEAL Team Six sun yi nasarar kubutar da Philip Walton, ɗan ƙasar Amurka mai shekaru 27, wanda akayi garkuwa dashi aka boye Najeriya.

Dakarun sojin Amurka sun kuɓutar dashi ba tare da samun ko ƙwarzane ba.

KU KARANTA KUMA: Allah ka hanemu da taurin kai, izza da jin babu wanda ya isa ya fada mana mu ji – Ali Nuhu

Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce ƙasar Amurka ta samu izinin Najeriya kafin ceto ɗan ƙasarta a arewacin Najeriya.

Ya faɗi hakan ne ga manema labarai a ginin Majalisa a Abuja jim kaɗan bayan kammala kare kasafin kuɗin ma'aikatar tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel