PTF ta ce Gwamnati ta ware N50b domin a rika gwajin COVID-19 a jihohi

PTF ta ce Gwamnati ta ware N50b domin a rika gwajin COVID-19 a jihohi

- Gwamnatin Tarayya ta hada-kai da Gwamnoni da nufin yakar Coronavirus

- Kwamitin PTF ya ce zuwa yanzu sun ba Gwamnonin jihohi Naira biliyan 50

- Sani Aliyu ya yi kira ga Gwamnoni su yi amfani da kudin wajen yin gwaji

Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 a Najeria, Dr. Sani Aliyu ya ce an ba jihohin kasar nan Naira biliyan 50.

Dr. Sani Aliyu ya ce gwamnatin tarayya ta bada wannan kudi ne domin a samu damar kara yi wa jama’a da dama gwajin kwayar cutar COVID-19.

Rahoton ya bayyana cewa Sani Aliyu ya yi wannan bayani ne lokacin da kwamitin PTF ya zauna da manema labarai ranar Talata a garin Abuja.

KU KARANTA: Najeriya ta karbi rigakafin COVID-19 daga ƙasar Rasha

Aliyu a madadin kwamitin PTF, ya yi kira ga gwamnoni su yi amfani da kudin da ke hannunsu wajen yin abin da gwamnatin tarayya ta bukata.

“Jihohi sun samu kaso mafi tsoka na kudin PTF. A yau, an ba su Naira biliyan 50.” Inji Sani Aliyu.

Ya ce: “Don haka mu na da halin da za mu kara yawan gwaje-gwaje a jihohi, da kuma karin bibiya.

Shugaban kwamitin na PTF ya jaddada bukatar samun kudi domin yaki da cutar COVID-19, ya ce har yanzu ba a fara hangen karshen annobar ba.

KU KARANTA: Minista ya yi gumi a gaban Sanatoci wajen kare kasafin kudin 2021

PTF ta ce Gwamnati ta ware N50b domin a rika gwajin COVID-19 a jihohi
Shugaban PTF, Sani Aliyu Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Sani Aliyu ya kuma bayyana cewa an soma yin gagarumin gwajin kwayar Coronavirus a makon nan.

“A wannan makon aka kara yawan wadanda ake yi wa gwajin COVID-19 a kasar nan. Mu na taya Abuja da Legas murnar yi wa jama’a da-dama gwaji.”

“Asali ma, a Abuja an yi 2% na wadanda mu ka tanada gwaji. Jihohi uku sun kama hanya – Filato, Gombe, da Ribas.” Aliyu ya ce jihohin sun kai 50%.

Kun ji cewa za a iya sake haramtawa Bayin Allah fita a Legas saboda dawowar Coronavirus kamar yadda Gwamnatin Legas ta bayyana a jiya.

Idan aka cigaba da saba doka, gwamnati za ta sa takunkumi da sauran matakan yaki da COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel