Idan ana watsi da dokokin COVID-19, za ta iya kai wa a rufe Legas inji Abayomi

Idan ana watsi da dokokin COVID-19, za ta iya kai wa a rufe Legas inji Abayomi

- Gwamnatin Legas ta ja kunnen Mazauna jihar game da bin dokokin Coronavirus

- Kwamishinan lafiya na Legas ya ce idan COVID-19 ta cika yaduwa, za a rufe gari

- Kwanakin baya gwamnati ta garkame mutane a gida, hakan ya taba tattalin arziki

Gwamnatin jihar Legas na iya sa sabuwar dokar hana fita da ma wasu tsauraran matakai idan aka samu barkewar sababbin masu dauke da cutar COVID-19.

Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba, 2020.

Rahoton ya ce wannan sanarwa ta fito ne daga bakin darektan yada labarai na ma’aikatar lafiyar jihar Legas, Tunbosun Ogunbanwo a ranar Talata da rana.

KU KARANTA: Abin da Trump ya tambayi Malaman asibiti da ya ke jinyar COVID-19

Tunbosun Ogunbanwo ya fitar da wani jawabi da ya yi wa take da ‘Lagos calls for precautions against second wave of COVID-19’, ya ce cutar ta na nan.

Gwamnatin jihar Legas ta na tsammanin annobar Coronavirus za ta sake barkowa a wani karon na biyu, don haka ta fara yin tanadi ko da hakan ya faru.

Kwamishinan kiwon lafiya na gwamnatin Legas, Farfesa Akin Abayomi ya ce kasashe da-dama sun ga bukatar sake turke jama’a a gida domin yakar cutar.

Sai dai hana mutane fita ya na da mummunan tasiri ta bangaren zamantake wa da tattalin arziki.

KU KARANTA: Jami'ar ABU Zaria ta samo maganin cutar COVID-19

Idan ana watsi da dokoki COVID-19, za ta iya kai wa a rufe Legas - Abayomi
Farfesa Akin Abayomi ya na jawabi
Asali: UGC

Kwamishinan ya yi gargadi cewa watsi da dokoki da matakan yaki da cutar COVID-19 da jama’a su ke yi, ya na jefa daukacin al’umma cikin danyar barzana.

“Gwamnatin Legas ta na fada da babbar murya cewa a rika bin ka’idoji yaki da COVID-19 domin gujewa abin da zai jawo a sake rufe gari.” Inji Akin Abayomi.

A watannin baya kun ji cewa wani rahoto mai ban kyama da aka fito da shi ya nuna cewa kasar Sin ta boye wa Duniya gaskiyar lamarin cutar COVID-19.

Wannan rahoto da ‘Five Eyes’ ta fitar ya bayyana cewa Sin ta yi wa Duniya karya game da yadda ake kamuwa da cutar COVID-19 tsakanin mutum da mutum.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng