Hotuna: Shekau ya saki sabon bidiyo tare da kananan yara da ya horar, ya aike sako
- Abubakar Shekau, shugaban kungiyar ta'addancin Boko Haram ya saki sabon bidiyo
- A sabon bidiyon, an ga Shekau tare da wani karamin yaro dauke da miyagun makamai
- Kamar yadda aka ji yaron yana cewa, ya sha alwashin ganin bayan "kafirai"
Shugaban mayakan ta'addanci na Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon bidiyo inda ya sha alwashin cigaba da barnar da yake yi.
Kamar yadda jaridar HumAngle ta wallafa, a sabon bidiyon an gan shi tare da wani karamin yaro rike da makamai inda ya ke barazanar ci gaba da yakar "kafirai".
A kwanakin baya ne jaridar HumAngle ta wallafa yadda kungiyar ta'addancin ke horar da kananan yara a wani sabon bidiyo da Boko Haram ta saki.
Wannan lamarin ya matukar daga wa jama'a hankali ganin cewa, za a saka wa kananan yara akidar rikau tare da ta'addanci tun kafin su san me ce ce rayuwa.
Wannan sabon bidiyon da ya fita yana sake jaddada lamarin da aka gani a wancan tsohon bidiyon.
Kungiyar ta'addancin Boko Haram ta kasance tana cin karenta babu babbaka tun a shekarar 2009.
KU KARANTA: EndSARS: Kashe 'yan sanda babban abun Allah wadai ne - El-Rufai
KU KARANTA: Karuwa ta kai wa magidanci 'yan sanda saboda ya kwace iPhone 11 da ya siya mata
A wani labari na daban, rundunar soji ta Operation Whirl Stroke ta samu nasarar halaka wasu 'yan bindiga, kwato miyagun makamai da kuma wasu kwayoyi a jihar Benue.
A sakamakon cigaban kokarin dakarun sojin Najeriya na ganin bayan 'yan bindiga da sauran miyagun al'amura a fadin kasar nan, rundunar Operation Whirl Stroke ta halaka 'yan bindiga biyu a jihar Nasarawa.
Rundunar hadin guiwa ta fita sintiri a ranar 18 ga watan Oktoban 2020 a kauyukan Kango da Adumata inda ta tarar da wasu 'yan bindiga.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng