Kudu maso gabas ya kamata su fito da Shugaban Najeriya inji Hon. Chukwu

Kudu maso gabas ya kamata su fito da Shugaban Najeriya inji Hon. Chukwu

- Victor Chukwu ya shiga sahun masu kiran a bar Ibo su nemi mulki a zaben 2023

- ‘Dan Majalisar ya ce yadda Fulani da Yarbawa su ka yi mulki, to saura Inyamuri

- Chukwu ya ce babu dalilin da zai sa a hana Ibo takarar shugaban kasa tun 1999

Victor Chukwu mai wakiltar mazabar Ezza ta Arewa a majalisar dokokin jihar Ebonyi, ya yi hira da jaridar Punch, inda ya yi magana game da siyasar Najeriya.

Hon. Victor Chukwu ya tabo maganar sauyin-shekar gwamna Dave Umahi wanda ake rade-radin zai fice daga jam’iyyar PDP, ya nemi yin takarar shugaban kasa.

Chukwu ya ce idan har PDP ta ki fito da ‘dan takarar shugaban kasarta daga yankin Kudu maso gabas a zaben 2023, jam’iyyar za ta gamu da kalubalen gaske.

KU KARANTA: ‘Yan siyasa 11 da ake yi wa hangen zama shugaban kasa a 2023

“Hadarin hakan ya na da girma, ba zan iya cewa kaza-da-kaza ba yanzu. Dalilin kuwa shi ne, ni shugaba ne a jam’iyya. Akwai tsarin shugabanci.” Inji Chukwu.

‘Dan majalisar ya ce: “Na tabbata abin ba zai yi kyau ba, asarar da za ayi ta na da yawa.”

Game da hana yankin takarar shugaban kasa, Chukwu ya ce: “Ban san abin da ya sa su ke yi wa yankin Kudu maso gabas haka ba. Babu dalilin cigaba da haka.

Honarabul Victor Chukwu ya ce: “Idan Bayarabe zai yi mulki a zauna lafiya, Fulani ya yi kalau, ‘Dan Ijaw ya yi mulki kalau, Mutumin Ibo ma zai iya yin haka.”

KU KARANTA: 2023 lokacinmu ne ba na kowa ba – Ndigbo sun fadawa Yarbawa da ‘Yan Arewa

Kudu maso gabas ya kamata su fito da Shugaban Najeriya inji Hon. Chukwu
Gwamnan Ebonyi Hoto: fmic.gov.ng/umahi-converts-states-moribund-five-star-hotel-to-varsity-faculty
Asali: UGC

“Babu wadanda su ka fi mu daraja a kasar nan, a yawan jama’a, kaifin basira.” Don haka jagoran na jam’iyyar PDP a Ezza ya ce lokaci ya yi da Ibo zai yi mulki.

A game da sauya-shekar gwamna Umahi, ya ce: “Da farko dai gwamna ba ya bukatar sa hannun wani ko amince wa kafin ya fice daga PDP ya jarraba sa’arsa."

“Ya na da dama a matsayinsa na ‘dan kasa ya sauya-sheka ko ya tsaya a jam’iyyarsa.” Inji sa.

Kwanakin baya kun ji cewa jihohin Anambra da Ebonyi su na so jam'iyyar PDP ta tsaida ‘dan takararta na zaben shugaban kasa a 2023 daga Kudu maso Gabas.

Jagororin PDP su na ganin cewa ya kamata ayi la'akari da hidimar da su ka yi wa jam'iyya a baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng