Da izinin gwamnati sojojin Amurka suka kai hari kan 'yan bindiga a arewacin Nigeria - Minista

Da izinin gwamnati sojojin Amurka suka kai hari kan 'yan bindiga a arewacin Nigeria - Minista

- Da sanyin safiyar ranar Asabar ne sojojin kasar Amurka suka kai hari a kan 'yan bidiga a arewacin Najeriya

- Sun kai harin ne domin kubutar da wani Ba-Amurke da aka yi garkuwa da shi

- Ministan tsaro na kasa, Bashir Magashi, ya yi karin bayani dangane da zargin cewa sojojin Amurka sun yi kuste zuwa cikin Najeriya

Sojojin Amurka na tawagar SEAL Team Six sun yi nasarar kubutar da Philip Walton, ɗan ƙasar Amurka mai shekaru 27, wanda akayi garkuwa dashi aka boye Najeriya.

Dakarun sojin Amurka sun kuɓutar dashi ba tare da samun ko ƙwarzane ba.

Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce ƙasar Amurka ta samu izinin Najeriya kafin ceto ɗan ƙasarta a arewacin Najeriya.

Ya faɗi hakan ne ga manema labarai a ginin Majalisa a Abuja jim kaɗan bayan kammala kare kasafin kuɗin ma'aikatar tsaro.

Wannan yazo ne bayan kwanaki uku da ceto ɗan ƙasar Amurka Philip Walton da sojojin ruwa na Amurka wanda akafi sani da SEAL Team Six Suka gudanar.

Babban mai magana da yawun Hukumar tsaron ƙasar Amurka a Pentagon, Jonathan Hoffman, ya ce sojojin Amurka sun gudanar da atisayen da safiyar ranar Asabar 31 ga watan Oktoba.

KARANTA: Sun kashe sojoji, sun kashe 'yan sanda - Wike ya zayyana irin barnar da IPOB suka yi a Ribas

"Babu jami'in ƙasar Amurka da ya samu rauni yayin atisayen. Mun yabawa Najeriya bisa tallafa mana yayin gudanar da atisayen", a cewarsa.

Da izinin gwamnati sojojin Amurka suka kai hari kan 'yan bindiga a arewacin Nigeria - Minista
Ministan tsaro Bashir Salihi Magashi
Asali: Facebook

Martanin minista Magashi yazo ne lokacin da ake raɗe-raɗin ko ƙasar tayi fatali da kimar Najeriya ta hanyar shigowa ba bisa ƙa'ida ba don gudanar da atisayen ceto, batun da yace ba dai-dai bane.

KARANTA: 'Yan sandan kasar Italy sun kama 'Sarkin Ferrara' da sauran wasu 'yan Nigeria 72

"Gwamnatin Amurka ta tuntuɓi gwamnatin Najeriya kuma ta samu sahalewar gudanar da atisayen."

"Ba wani abin aiibu bane kasar Amurka ta nemi izinin takwararta Najeriya kafin ta gudanar da atisayen ceto.

"Hakan ma ƙara ɗanƙon zumunta tsakanin ƙasashen shi yasa muka bari hakan ta kasance," a cewar Magashi.

Legit.ng Hausa ta wallafa cewa a ranar Talatar makon jiya ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da wani Ba-Amurke a jamhuriyar Nijar tare da shigowa da shi Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel