'Yan sandan kasar Italy sun kama 'Sarkin Ferrara' da sauran wasu 'yan Nigeria 72

'Yan sandan kasar Italy sun kama 'Sarkin Ferrara' da sauran wasu 'yan Nigeria 72

- Halayyar da wasu 'yan Najeriya ke nunawa a kasashen ketare ta jawo zubewar mutunci da darajar bakin mutum a idon duniya

- Ƴansandan ƙasar italiya sun kai farmaki kan shugaban gungun ƴan ƙungiyar matsafa ta asalin 'yan Najeriya

- An kama shugaban mai suna Emmanuel Okenwa, da sauran ƴan tawagarsa su 72

'Yan sanda a ƙasar Italiya sun kama mutum saba'in da da uku (73) ƴan ƙungiyar matsafa kuma ƴan asalin Najeriya.

Shi ma Shugaban ƙungiyar matsafan mai shekaru 50, Emmanuel Okenwa, ya shiga hannu.

Jami'an yan sanda sama da 200 ne suka gudanar da atisayen kama matsafan a wani samame da suka kai mafakarsu a garin Turin da Ferrara.

Jaridar ƙasar Italiya mai suna ANSA ta rawaito cewa ƴan sanda sun kama mambobin ƙungiyar matsafa ƴan asalin Najeriya da ake kira da sunan "Arobaga Vikings" ko Norsemen Kclub International.

Akwai ƙungiyar acikin birane da manyan garuruwan ƙasar Italiya daban-daban.

KARANTA: Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi shagube ga masu tsine mata a Masallatai

Tuni shugabannin ƙungiyar, wadanda suka ƙware a harkar karuwanci da safarar ƙwayoyi, suka shiga komar jami'an tsaron kasar Italiya.

'Yan sandan kasar Italy sun kama 'Sarkin Ferrara' da sauran wasu 'yan Nigeria 72
'Yan sandan kasar Italy sun kama 'Sarkin Ferrara' da sauran wasu 'yan Nigeria 72 @TheNation
Asali: Twitter

Wadanda aka kama sun haɗa da 'Boogye', mai sana'ar kunna faifan sautin Afirka, wanda kuma ya sakawa kansa suna"Sarkin Ferrara."

Daga cikin mutanen da aka kama, 31 an kama su ne a Ferrara.

Tuni har an gurfanar da mutane 43, wadanda suka haɗar da mata masu sana'ar karuwanci, a gaban kotu.

Bincike farko na alƙali Gianluca Petragnani Gelosi na garin Bologna ya gano cewa shirin masu laifin shine su rushe tarihin duk wasu laifukan ƴan Najeriya sannan su maye gurbinsu da manyan laifuka.

KARANTA: Gwanda lalatattun 'yan sanda da kwararrun 'yan ta'adda - Gwamna Abdulrazaq

Ministan harkokin cikin gida a Italiya Luciana Lamorgese ya ce ƴan sanda zasu cigaba da kare ƴanƙasa daga kungiyoyin masu aikata laifuka koda kuwa suna halin ko ta kwana a tsakiyar annobar COVID-19.

A wani labarin makamancin wannan ƴansanda a kasar Italiya sun gurgunta ƙungiyar Ndrangheta Mafia wacce ke ƙasashe daban-daban na duniya.

Ƴan sandan, a ranar a Alhamis, sun kwace Yuro miliyan 50 da dukiya mai yawa mallakar ƴan kasuwa guda uku a Reggio Calabria wanda suke da haɗi da kungiyar Ndrangheta mafia.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel