Sun kashe sojoji, sun kashe 'yan sanda - Wike ya zayyana irin barnar da IPOB suka yi a Ribas

Sun kashe sojoji, sun kashe 'yan sanda - Wike ya zayyana irin barnar da IPOB suka yi a Ribas

- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya tashi haikan domin murkushe 'yan kungiyar IPOB da ke tayar da kayar baya a Fatakwal

- Wike ya sanar da cewa mambobin kungiyar IPOB sun kashe sojoji da 'yan sanda tare da tafka barna mai yawa a jihar Ribas

- Tuni gwamna Wike ya murza gashin baki tare da sanar da IPOB cewa ba zai yarda su yi amfani da jiharsa wajen assasa muguwar manufarsu ba

Kungiyar masu fafutikar kafa ƙasar Biyafara ta 'yan kabilar Igbo (IPOB) sun kashe sojoji 6, ƴansanda 4 har lahira a jihar Rivers, inji Gwamna NyesomWike na jihar Rivers.

Gwamnan Wike ya bayyana irin ɓarnar da wasu matasa da ake zargin ƴan ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biyafara(IPOB) da sunan zanga-zangar kawo ƙarshen SARS(#EndSARS).

A cewar Wike; "haramtacciyar ƙungiyar IPOB ta kashe sojoji shida 6 da ƴansanda 4 a jihar Rivers".

Wike ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da mai bashi shawara na musamman akan harkar yaɗa labarai, Kelvin Ebiri, ya sawa hannu lokacin da gungun editocin Najeriya suka kai masa ziyara a gidan gwamnati dake birnin Fatakwal.

KARANTA: Tirkashi: An samu bindigu 65 a wurin masu laifi 157 da aka kama a Kaduna

Gwamna Wike ya ce zanga-zangar kawo karshen SARS #EndSARS ta lumana ce kafin ƴan haramtacciyar ƙungiyar fafutikar kafa ƙasar Biyafara (IPOB) su kwace ragamara a jihar Ribas.

"Haramtaciyyar kungiyar fafutikar kafa kasar Biyafara IPOB ta haddasa asarar rayuka da dukiya mai yawa a jihar Rivers", a cewarsa.

Sun kashe sojoji, sun kashe 'yan sanda - Wike ya zayyana irin barnar da IPOB suka yi a Ribas
Nyesom Wike Premium Times
Asali: Facebook

Sannan ya cigaba da cewa; "Ƙungiyar IPOB ta zama sanadiyyar mutuwar jami'an sojoji guda shida da ƴansanda huɗu ta hanyar kashe su har lahira."

Gwamna Wike ya ce bai kamata al-ummar Igbo su bari masu laifi ƴan ta'adda su zama masu magana a matsayinsu ba.

KARANTA: 'Yan sandan kasar Italy sun kama 'Sarkin Ferrara' da sauran wasu 'yan Nigeria 72

Zanga-zangar lumana ta ENDSARS ta birkice zuwa kazamin rikici da ya zama silar rasa dumbin rayuka a jihohin Najeriya.

Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa rundunar 'yan sanda Najeriya da ke kowacce jiha na cigaba da sanar da kama matasan da ake zargi da fakewa da zanga-zangar ENDSARS wajen tafka barna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng