Jami’an tsaro sun damke Matashin da ya hallaka Budurwa a Jihar Ogun
- Ana zargin wani Matashi da laifin kashe Budurwa a dakin otel a jihar Ogun
- Wannan mutumi da ake zargi ya ce ya na cikin dukan Budurwar sai ta mutu
- Daga nan ya sadada ya bar gawar ta, sai daga baya ma’aikatan otel su ka lura
Vanguard ta fitar da rahoto cewa jami’an ‘yan sanda sun cafke wani mutumi mai shekara 31 da laifin yi wa buduwarsa mai shekara 26 kisan gilla.
Dakarun ‘yan sandan na jihar Ogun sun kama wannan Bawan Allah, Rexlawson Jonson, a dalilin zarginsa da ake yi da kashe sahibarsa a dakin otel.
Wannan mutumi da ake zargi da kisan-kai ya fito ne daga Ebonyi. Jaridar ta ce ya shiga hannun hukuma a ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoba, 2020.
KU KARANTA: EndSARS: Gwamnonin Arewa sun zabi Sarkin Zazzau ya zauna da Matasa
Kakakin ‘yan sandan jihar Ebonyi, DSP Abimbola Oyeyemi, ya fitar da jawabi, ya ce rundunar ‘yan sanda ta yi nasarar yin ram da Rexlawson Johnson.
‘Yan sanda sun cafko Rexlawson Jonson bayan Manajan wani otel da ake kira ‘Molayo Hotel’ mai suna Adebayo Aladesuyi ya kai kara gaban jami’ai.
Mista Aladesuyi ya shaida wa jami’an tsaro cewa yayin da su ke zagayen dakunan otel ne su ka ga gawar wata Budurwa da aka yi wa rauni a wuya.
“A dalilin karar da aka kawo, DPO na yankin Ibafo, Csp Jide Joshua ya jagoranci tawagarsa inda su ka kai gawar zuwa dakin ajiye gawa domin ayi bincike.”
KU KARANTA: Banbami ko ta ina yayin da kamfanonin wuta su ka kara farashi
Da aka yi bincike sai aka gano cewa marigayiyar ta shigo otel ne tare da wani mutumi wanda ake zargin ya tsere bayan ya yi nasarar aikata zuwa barzahu.
Kwamishinan ‘yan sanda na Ogun, CP Edward Awolowo Ajogun, ya ce sun kamo wannan mutumi, kuma ya bada labarin yadda ya kashe ta duka.
Johnson ya ce sun sabani da marigayiyar har ya kai ga duka, ya ce ya na cikin dukanta, ta mutu.
Idan mu ka koma kasar waje, za mu ji cewa jami’an ‘Yan Sanda sun yi awon-gaba da Ryan Giggs bayan ya mangari budurwarsa da su ke tare a Manchester.
Tsohon rauraron ‘Dan wasan kwallon kafa, Giggs ya shiga hannun Jami’an tsaro ne a ranar Lahadi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng