Taron NGF: Sarki Ahmad Bammali zai jagoranci kwamitin matasa da kungiyoyi

Taron NGF: Sarki Ahmad Bammali zai jagoranci kwamitin matasa da kungiyoyi

- An nada Kwamitoci bayan taron da Gwamnonin Arewa su ka yi a Kaduna

- Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ne aka zabi ya rike kwamitin Matasa

- Kusan wannan ne aikin farko da Sarkin zai yi tun bayan hawa gadon mulki

A ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba, 2020, gwamnonin Arewa da manyan gwamnatin tarayya su ka yi wani muhimmin taro a jihar Kaduna.

Legit.ng ta samu labarin matsayar da aka cinma bayan wannan zama, daga ciki za ayi amfani da Sarakunan yankin wajen kawo zaman lafiya.

Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli da takwaransa na kasar Lafia, Sidi Bage Muhammad su na cikin wadanda aka zaba su rike kwamitocin.

KU KARANTA: Arewa: IGP, Gwamnoni, Sarakuna, Ministoci sun shiga muhimmin taro

Kungiyar NGF ta zabi Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya shugabanci kwamitin da zai yi aiki da matasa da duk kungoyoyi masu zaman kansu.

‘Yan wannan kwamiti za su hada da wakili guda daga kowane yanki na kasar, da kuma wakilan matasa da nakasassu daga jihohin yankin Arewa.

Bayan haka mata da ‘yanmata za su samu wakili guda daga kowace shiyya. Kwamitin zai samu wakilcin malaman kiristoci da musulunci.

Ragowar ‘yan kwamitin su ne ‘yan kasuwa da kuma wakilin sufeta janar na ‘yan sanda.

KU KARANTA: An ceto wadanda aka yi garkuwa da su a masallaci a Nasarawa

Taron NGF: Sarki Ahmad Bammali zai jagoranci kwamitin matasa da kungiyoyi
Ahmad Bammali tare da wasu Sarakuna a taro Hoto: Twitter/Gov. Kaduna
Asali: Twitter

Kamar yadda kungiyar gwamnonin jihohin Arewa ta bada umarni, wannan kwamiti da takwarorinsa za su fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnonin sun yaba da kokarin da sarakunan gargajiya su ke yi wajen kawo zaman lafiya ganin abin da ya faru wajen zanga-zangar #EndSARS.

A jiya kun ji cewa Gwamnonin Arewa 19 da manyan Sarakunan yankin sun sa labule a Jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufai.

Ibrahim Gambari, IGP, Ministoci da ‘Yan Majalisa su na cikin wadanda ake yi wannan zama da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng