FAW ta tabbatar ana binciken Kocin kasar Wales, Ryan Giggs a Birtaniya
- Ryan Giggs ya fada tarkon Jami’an tsaro ranar Lahadi a kasar Ingila
- Ana zargin tsohon ‘dan kwallon ne da doke wata mata mai shekaru 30
- Kocin ya buga wa Manchester United kwallo na shekaru masu yawa
Rahotanni daga wasu jaridun kasar Ingila sun ce mai horas da ‘yan wasan kwallon kafan kasar Wales, Ryan Giggs ya fada hannun hukuma.
A ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba, aka samu labarin cewa jami’an tsaro sun cafke Ryan Giggs bisa zarginsa da ake yi na kai wa wani farmaki.
Hukumar da ke kula da kwallon kafa a kasar Wales ta fitar da jawabi, ta ce lallai ta samu labarin abin da ya faru da kocin ‘yan wasan kwallonta.
KU KARANTA: COVID-19 ta harbi 'dan wasan Liverpool
Ta ce: “FAW ta na sane da zargin da ake yi wa kocin ‘yan kwallon kasar Wales, Ryan Giggs. FAW ba za ta ce komai game da lamarin ba a yanzu.”
Jaridar Sun ta ce an kira ‘yan sanda gidan Ryan Giggs mai shekaru 46 a Duniya. Wannan ya faru da yammacin ranar Lahadin nan da ta wuce.
Wata majiya daga Ingila ta shaida cewa: "An cafke Giggs, an yi masa tambayoyi bisa zarginsa da ake yi na kai wa wata hari, tare da ji mata rauni.”
Majiya daga ‘yan sandan Manchester ta ce “An kira wa Giggs ‘yan sanda a ranar Lahadi da kimanin karfe 10:05 bayan shigar da karar hayaniya.
KU KARANTA: Ganduje ya dauko hayar Bature ya rike Kano Pillars
“Wata mai shekaru kimanin 30 ta samu kananan rauni, amma ba su kai a duba ta a asibiti ba.”
Jami’an tsaron sun tabbatar da: “An kama mutum mai shekaru 46, da zargin aikata laifuffukan da su ka saba wa sashe na 47 da 39 na kai farmaki.”
Giggs ya buga wa Manchester United, sannan ya yi aiki da kungiyar, ya kuma sa rigar kasar Wales, kafin a zabe shi a matsayin kocin ‘yan wasan kasar.
Daga baya 'dan wasan tsakiyan ya musanya wannan rahoto, ya ce bai yi ritaya a kasarsa ba.
Asali: Legit.ng