IPPIS: Kudin biyan albashin Ma’aikata a MDAs sun kare kafin karshen shekara
- Wasu Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Tarayya sun daina biyan albashi
- Kudin da aka ware domin batarwa da biyan albashi a MDA kusan 430 sun kare
- A daidai wannan lokaci ne aka ji labarin NNPC ta kashe N375 a kan ma’aikanta
Vanguard ta ce akalla ma’aikatu da hukumoni 428 a gwamnatin tarayya sun karar da kudin batar wa da aka ware masu a cikin kasafin shekarar 2020.
A halin yanzu ma’aikata da-dama ba su karbar albashi saboda wannan matsala. Kason kudin wadannan ma’aikatu a asusun IPPIS ya kare kar-kaf.
Ana adana kudin biyan albashi ne a cikin asusun IPPIS da ke ofishin babban akawun gwamnati.
KU KARANTA: Malaman Jami'a 57, 000 sun shiga IPPIS - Minista
Wani jami’in gwamnatin tarayya da ya zanta da ‘yan jarida a boye ya bayyana cewa abin mamaki ne kudin biyan albashi su kare kafin karshen shekara.
Jami’in ya ce dole shugabannin wadannan hukumomi da matsalar ta shafa su yi bayanin ainihin abin da ya faru da kudin da aka ware masu a farkon bana.
Rahoton ya ce a dalilin haka, ma’aikatan gwamnati sun shiga halin ni–‘yasu. A wasu hukumomin, ma’aikata ba su iya zuwa ofis saboda rashin kudi.
A lokacin da ma’aikatan gwamnatin tarayya su ke fama da rashin albashi, rahotanni sun nuna NNPC ta kashe Naira biliyan 375 wajen biyan albashi a bara.
KU KARANTA: Banbami ko ta ina yayin da kamfanonin wuta su ka kara farashin lantarki
Ma’aikatan NNPC sun ci Naira biliyan 357.098 a matsayin albashi, alawus da sauran hakkoki a 2019 kamar yadda alkaluman da hukumar man ta fitar ya nuna.
An samu karin Naira biliyan 14.74 a kan abin da hukumar ta kashe a 2018. Sai dai yanzu NNPC ta dauki sababbin ma’aikata 1, 050, ko da an kuma sallami wasu.
Abin da NNPC ta kashe a wajen biyan albashi ya fi karfin kasafin kudin jihohi irinsu Delta, Kano, Kaduna, Borno, Sokoto, Edo, Abia, Ribas, jihar Filato da sauransu.
Shugaban kasar ya kara wa malaman shekarun aiki daga 35 zuwa 40 kafin su yi ritaya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng