Aisha Buhari za ta kafa cibiyoyin binciken cutar daji a duka yankunan kasar nan

Aisha Buhari za ta kafa cibiyoyin binciken cutar daji a duka yankunan kasar nan

- Aisha M. Buhari ta ce za ta gina dakunan gwajin cutar daji a yankunan Najeriya

- Uwargidar shugaban Najeriya ta na ganin hakan zai taimaka wajen yakar cutar

- Hadimar matar shugaban kasar, Dr. Hajo Sani ce ta bayyana haka a taron NCWD

Yayin da ake karkare shirye-shiryen watan wayar da kai game da cutar daji wanda aka fi sani da kansa, uwargidar shugaban Najeriya ta yi hobbasa.

This Day ta ce Aisha Muhammadu Buhari ta bada sanarwar maida hankali wajen awo domin gano masu dauke da wannan mummunar cuta a Najeriya.

Aisha Buhari ta ce za ta gina wuraren awo da gwajin cutar daji a duka yankunan shida da ke kasar.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta yi shagube game da halin rashin tsaro

Uwargidar shugaban kasar Najeriyar ta bayyana haka ne a lokacin da ta halarci bikin kaddamar da shirin wayar da kan mata a game da ciwon daji.

Hukumar kula da cigaban mata na kasa, NCWD ta shirya wannan taro domin a fadakar da mata a kan cutar dajin mama da ta mahaifa da ke damunsu.

Mai taimaka wa mai dakin shugaban kasar a harkokin gudanar wa da sha’anin mata, Hajo Sani, ta wakilci Aisha Muhammadu Buhari wajen taron a Abuja.

Dr. Hajo Sani ta ce Hajiya Aisha Buhari ta riga ta bude irin wannan cibiya a jihar Kano. Za a gina saura a yankunan Arewa ta tsakiya, Arewa maso Kudu.

KU KARANTA: Gwamnan Legas ya ce zai ba Matasa da su kammala makaranta aiki

Aisha Buhari za ta kafa cibiyoyin binciken cutar daji a duka yankunan kasar nan
Aisha Buhari Hoto: fmic.gov.ng
Asali: UGC

Bayan haka za a gina irin wannan daki domin gwajin cutar daji a Kudu maso gabas, Kudu maso yamma da kuma yankin Kudu maso kudancin Najeriya.

Sani ta ce amfanin dakunan gwajin shi ne wayar da kan matan karkara game da hadarin cutar.

A makon jiya kuma aka ji cewa Najeriya ta sha alwashin ganin Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta hau kujerar kungiyar WTO, duk runtsin da za a iya fuskanta.

Gwamnatin kasar za ta dage kan ‘yar takararta ko ana ha-maza, ha-mata inji ma’aikatar kasar waje.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel