Zaben shugaban kasa: Zan sake kafa tarihi a kasar Amurka - Trump
- A yau, Talata, uku ga watan Nuwamba ake gudanar da zaben kujerar shugaban kasa a kasar Amurka
- Amurkawa na da zabin kada kuri'a ga daya daga cikin 'yan takara guda biyu; Donald Trump da Sanata Joe Biden
- Trump ya na takara ne a karkashin inuwar jam'iyyar 'Republican' yayin da Biden ke takara a karkashin inuwar jam'iyyar 'Democrat'
Shugaban ƙasa Donald Trump ya jaddada cewa zai sake kafa tarihi a yayin da Amurkawa ke jefa ƙuri'un su a ranar Talata.
A ranar Litinin ne Trump ya kammala rufe yaƙin nenan zaɓensa a cikin ɗumbin cikowar jama'a a jihohi huɗu na Amurka.
Trump ya nanata maganar aringizon ƙuri'u da aka yi masa.
Da yake jawabi a gaban jama'ar da safiyar ranar Talata a Grand Rapids,Michigan,in zaku tuna nan ne wurin da Trump ya kammala yaƙin neman zaɓen sa a shekarar 2016.
KARANTA: Najeriya ta ƙara faɗawa tsilla-tsilla sakamakon faɗuwar farashin ɗanyen man fetur
Trump mai shekaru 74 ɗan takarar jam'iyyar Republican ya ce zai sake komawa a karo na biyu.
"Zamu sake samun kyakkyawar nasara a wannan zaben," Trump ya gayawa taron jama'ar Michigan, wadanda suka yi ihu tare da hada bakin wajen yi masa jinjinar "muna sonka, muna sonka"
"Zamu sake kafa tarihi a wani karon" a Trump.
KARANTA: 2020: Yadda za a duba sakamakon jarrabar WAEC cikin sauki ta hanyar bin matakai 7
A ranar Asabar, 31 ga watan Okotoba, ne Legit.nga Hausa ta wallafa rahoton cewa an soke al-amurran yaƙin neman zaɓen Sanata Joe Biden ɗan takarar shugaban ƙasar Amurka a inuwar jam'iyyar Democrat sakamakon barazana daga magoya bayan shugaba Donald Trump.
Ƴan jam'iyyar Democrat sun ce an soke gangamin yaƙin neman zaɓen ne wanda aka shirya yinsa ranar juma'a a Pflugerville, wani gari a Texas, saboda dalilai na tsaro da shawarwari makamantan hakan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng