Najeriya ta ƙara faɗawa tsilla-tsilla sakamakon faɗuwar farashin ɗanyen man fetur.

Najeriya ta ƙara faɗawa tsilla-tsilla sakamakon faɗuwar farashin ɗanyen man fetur.

- Najeriya ta shiga tsaka mai wuya sakamakon faɗuwar farashin man fetur da kaso 3.43% zuwa Dala$36.64

- Ƙungiyar ƙasashe masu arziƙin man fetur (OPEC) ta ƙayyade adadin gangar ɗanyen man fetur da za'a fitar kullum zuwa miliyan 7.7 a kasuwar duniya

- Gwamnatin Najeriya na shirin ciyo bashi daga Asusun ajiya na duniya da kuma Bankin duniya sakamakon halin matsin tattalin arziƙi

Farashin ɗanyen man fetur na Brent ya faɗi da kaso 3.43%; zuwa Dala $36.64, a kan duk gangar ɗanyen man fetur a ranar litinin.

Hakan ya biyo bayan dokar kulle da wasu ƙasashen turai suka sake ƙaƙabawa don daƙile yaɗuwar cutar annobar Korona, wacce ta sake dawowa a karo na biyu.

Cutar COVID-19 tana yaɗuwa a sassa na duniya daban-daban inda masana kimiyya da ƙwararru a harkar lafiya ke gargaɗin ɓallewar cutar a karo na biyu.

Farashin ƙasar Amurka na WTI (West Texas Intermediate) shi ma ya faɗo da kaso 3.97% zuwa $34.37 a kan duk gangar ɗanyen man fetur.

KARANTA: Na yi aiki da Gowon, Buhari, da OBJ amma yanzu sai na roki abinci - Kaftin Mai ritaya

Raguwar kuɗin da ake samu daga cinikin ɗanyen man fetur, wanda ya kasance babban ɓangaren da yafi kowanne kawowa kasa kuɗin shiga, ya haddasa matsin tattaƙin arziƙi a karo na biyu cikin shekaru biyar.

Kazalika, dokar kulle da aka sa dominn daƙile yaɗuwar annobar Korona ta sake rage hada-hadar harkokin kasuwanci.

Najeriya ta ƙara faɗawa tsilla-tsilla sakamakon faɗuwar farashin ɗanyen man fetur.
Shugaban NNPC, Mele Kyari
Asali: UGC

Domin yaƙar ƙarancin kuɗin shiga daga ɓangaren man fetur, gwamnatin Najeriya na yunƙurin warware matsalar ta hanyar tattara kuɗaɗen shiga daga wasu ɓangarorin.

Gwamnati ta tunkari masu bayar da bashi kamar su Asusun lamuni na duniya (IMF), bankin duniya duniya da kuma Bankin cigaban Afirika (ADB) domin ƙarbar bashi.

KARANTA: 2020: Yadda za a duba sakamakon jarrabar WAEC cikin sauki ta hanyar bin matakai 7

Ana hasashen matsalar zata ƙara ta'azzara sakamakon niyyar ƙasar Libiya da Iraƙi na kawo ɗanyen man fetur ɗinsu kasuwar duniya.

Dokar hana tafiye-tafiye da kuma ragowar harkokin kasuwannci sune suka haddasa ƙarancin bukatar man fetur da makamantansa.

Ƙungiyar ƙasashe masu arziƙin man fetur (OPEC) da takwarorinta sun yanke shawarar rage adadin yawan adadin man fetur zuwa gangar ɗanyen man fetur miliyan 7.7 a kowacce rana don samun daidaito a kasuwar man fetur.

A makon jiya ne gwamnatin tarayya ta sanar da kaddamar da shirin bunkasa tattalin arziki.

A karkashin wannan shiri, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta fara biyan N30,000 ga masu sana'ar hannu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng