Kungiya ta bayyana jerin sunayen ‘yan siyasa 11 da take so su zama shugaban kasa a 2023
- Kungiyar Igbo for President Solidarity Group, karkashin jagoranci Dr. Olukayode Oshiariyo, ta nuna ra'ayinta na son ganin an mika shugabanci ga yanki kudu maso gabas a 2023
- A cewar kungiyar, tun 1999, kudu maso yamma, arewa maso yamma da kudu maso kudu ne suka samar da shugabannin kasa
- Ta baya wasu jerin 'yan siyasa goma sha daya da take ganin sun cancanci wannan kujera daga yankin kudancin kasar
Wata kungiyar Igbo mai suna Igbo for President Solidarity Group, karkashin jagoranci wani Bayarabe mai suna, Dr. Olukayode Oshiariyo, ta yi tsokai kan zaben 2023.
Sashin Linda Ikeji ya ruwaito cewa kungiyar ta bayyana wasu ‘yan siyasa 11 daga kudu maso gabas da “suka cancanci a gabatar da su a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023."
Da yake sanar da sunayen ‘yan siyasan Igbo a ranar Juma’a, 28 ga watan Agusta a Abuja, bayan taron kungiyar, shugabanta, Dr. Olukayode Oshiariyo, ya ce lokaci ya yi da kasar za ta samar da shigaban kasa daga kabilar Igbo.
"IPSC ta yanke shawarar cewa, wani mutum imma namiji ko mace daga kabilar Igbo zai zama shugaban kasar Najeriya.
“IPSC za ta yi wasu tuntube-tuntube a fadin yankunan shida, za ta ziyarci sarakunan arewa, sarakunan yarbawa, sarakunan Igbo da shuwagabanni, domin tattaunawa da duba halayya da mutuncin mutum goma sha bakwai da take ganin sun cancanta,” in ji shi.
Sunayen mutanen da kungiyar ta bayyana sun hada da, Dr Ogbonaya Onu, Peter Obi, Dr Chris Ngige, Rochas Okorocha, Dave Umahi, Orji Uzor Kalu, Ike Ekweremadu, Enyinnaya Abaribe, Ifeanyi Ugwuanyi, Ifeanyi Uba, and Kingsley Moghalu.
KU KARANTA KUMA: Ganduje ya nada sabbin alƙalai 6 a Kano (Sunaye)
“Tun 1999, kudu maso yamma, arewa maso yamma da kudu maso kudu ne suka samar da shugabannin kasa, bisa ga al’ada, ana mulkin karba-karba saboda daidaito da adalci kamar yadda yake a manufofin tarayya.
“Don haka, a 2023, ya kamata a duba yankin kudu maso gabas a matsayin yanki guda a yankin kudu da bata samar da wani shugaban kasa ba,” Oshiariyo ya kara da cewa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng