Anambra da Ebonyi su na so PDP ta tsaida ‘dan takara daga Kudu maso Gabas

Anambra da Ebonyi su na so PDP ta tsaida ‘dan takara daga Kudu maso Gabas

- Shugabannin PDP su na kiran a ba mutumin Ibo takarar Shugaban kasa a 2023

- PDP ta reshen Anambra da Ebonyi ta ce idan za ayi adalci, a ba yankinsu tikiti

- Ko da akwai sauran shekaru a gaba, an fara yakin neman zaben 2023 tun yanzu

Wasu shugabannin PDP su na kiran uwar jam’iyya ta tsaida kujerar ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 daga yankin Kudu maso gabas.

A ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba, jam’iyyar PDP na reshen Anambra da Ebonyi su ka fito su na neman a ba yankinsu tikitin zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta ce wannan kira ya zo ne jim kadan bayan majalisar dokokin jihar Ebonyi ta ba shugabannin PDP wa’adin a aba su tikitin.

KU KARANTA: Manyan Ibo sun fadawa ‘Yan siyasan Arewa da Yarbawa su hakura da 2023

Shugabannin rassoshin na Anambra da Ebonyi a Kudu maso gabashin Najeriya sun ce ba za su amince da wani shiri dabam da hakan ba.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘ya ‘yan jam’iyyar sun ba majalisar gudanarwa ta PDP watau NWC, mako guda domin ta cika mata sharudansu.

Jagororin jam’iyyar adawar sun ce idan har ba a biya masu bukatunsu ba, za su dauki mataki.

Shugaban PDP na jihar Ebonyi, Onyekachi Nwebonyi ya bayyana duk wannan a lokacin da ya gana da ‘yan jarida a ranar Talata da yamma.

KU KARANTA: Kungiyar Fulani za ta fallasa masu ta'adi da sunan Makiyaya

Anambra da Ebonyi su na so PDP ta tsaida ‘dan takara daga Kudu maso Gabas
Shugaban PDP na kasa Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: Twitter

Shi ma takwaransa na Anambra, Ndubuisi Nwobu, ya ce duk wani mutumin Ibo ya na jiran ya ga sun fito da shugaban kasan Najeriya a 2023.

Nwobu ya ce idan akwai adalci, duka manyan jam’iyyu su fito da wadanda za su rike masu tuta a zabe mai zuwa daga yankin Kudu maso gabas.

A makon nan ne ku ka ji cewa Akwai yiwuwar Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, ya koma APC. Umahi ya lashe duka zabensa ne a karkashin PDP.

Ana rade-radin Gwamna David Umahi zai sauya-sheka ne saboda takarar shugaban kasa a 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng