2023 lokacinmu ne ba na kowa ba – Ndigbo sun fadawa Yarbawa da ‘Yan Arewa

2023 lokacinmu ne ba na kowa ba – Ndigbo sun fadawa Yarbawa da ‘Yan Arewa

- Kungiyoyin Ibo sun fara buga tamburan yakin neman zaben 2023 tun a yanzu

- Wasu manyan yankin sun ce ya kamata Ibo ya yi mulki don Najeriya ta dinke

- Rabon mutumin Ibo da rike Najeriya tun Janar Aguiyi-Ironsi a shekarar 1966

Jagororin Ibo sun sanar da takwarorinsa da ke Arewa da Kudu maso yammacin Najeriya cewa su daina lissafin su za su sake karbar mulki a zaben 2023.

Jaridar Vanguard ta ce a kungiyoyin Ibo a karkashin Global Movement for Igbo President watau GLOMIP 2023 da Ohanaeze sun kira taron ‘yan jarida jiya.

Wannan kungiya da kuma Ohanaeze ta reshen Ingila da Ireland sun gabatar da bukatunsu gaban Duniya, daga ciki shi ne a canzawa tsarin kasar nan fasali.

KU KARANTA: Ana kiran tsohon Gwamnan Abi ya nemi mulki a 2023

Cif Chukwuemeka Ezeife ya bayyana cewa yanzu haka mutanen Ibo su na harin jerin wasu ‘yan siyasa da za su nemi takarar shugabancin kasa a zaben 2023.

Chukwuemeka Ezeife ya yi watsi da rade-radin cewa Ibo ba za su hada-kansu ba. Ya ce: “Za mu fito da wanda zai kaunaci Hausa, Yarbawa da Ibonsa.”

Tsohon gwamnan ya ce ba zai kama sunan wadanda za su yi masu takara ba tukuna. Sannan ya ce Najeriya ta fara samun matsala ne bayan juyin-mulkin 1966.

Shugaban Ohanaeze Ndigbo UK da Northern Ireland, Dr, Nnanna Elias Igwe ta bakin Mazi Godffrey Azu ya ce da Ibo za a gwabza a zabe mai zuwa.

2023 lokacinmu ne ba na kowa ba – Ndigbo sun fadawa Yarbawa da ‘Yan Arewa
Chukwuemeka Ezeife Hoto: saharareporters.com
Asali: Facebook

KU KARANTA: Abin da ya kamata ka sani a kan Gowon; Shugaban kasan 1966 - 1975

A jawabinsa, Elias ya ce: “Hanyar da za a lafar da kiran a barka kasa shi ne a mika wa Ibo mulki a 2023. Mu da ke ketare, ba za mu yi wasa a zaben 2023 ba.”

Ya ce: “Yadda za a kashe maganar raba Najeriya shi ne a ba mutumin Ibo shugabanci a 2023.”

A baya kun samu rahoto cewa ana rade-radin cewa Gwamnan Ebonyi David Umahi zai sauya-sheka a makon nan, gwamnan zai koma jam'iyyar APC.

Idan hakan ta tabbata, duka shugabannin kananan hukumomin jihar Ebonyi za su bi gwamnan zuwa APC, a wani yunkuri da ake gani na nema mulki a 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel