Sanwo-Olu ya bayyana shirin daukar Matasa 400 da zai koya wa sanin kan-aiki

Sanwo-Olu ya bayyana shirin daukar Matasa 400 da zai koya wa sanin kan-aiki

- Gwamnatin Babajide Sanwo-Olu za ta koya wa Matasa 400 aiki a Legas

- Wadanda za a dauka aiki za su rika samun na-kashewa N4000 duk wata

- Yetunde Arobieke ta ce wannan ya na cikin manufofin gwamnatin jihar

A yunkurinsa na rage rashin aikin yi a jihar Legas, gwamna Babajide Sanwo-Olu ya kirkiro tsarin da zai rage yawan marasa aikin-yi.

Gwamnatin Legas ta skawo tsarin da ake kira Graduates Internship Placement Programme (GIPP) wanda zai yi maganin zaman banza.

A wannan sabon shiri, za a horas da masu zaman kashe wando, a koya masu sana’o’Ii kamar yadda gwamnatin jihar Legas ta bayyana.

Vanguard ta rahoto kwamishinar samar da dukiya ta Legas, Yetunde Arobieke, ta na cewa wannan ya na cikin manufofin gwamnatinsu.

KU KARANTA: Marasa imani sun kashe ‘Dan Sanda bayan an datse masa mazakuta

Jaridar ta ce kwamishinar ta bayyana haka ne a wajen kaddamar da wannan shiri na GIPP, a ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba.

Yetunde Arobieke ya ce sun shigo da wannan tsari ne da nufin horas da matasa ta yadda za su samu saukin samun aikin yi nan gaba.

Gwamnatin Legas za ta horas da wadannan matasa 4, 000 da aikin hannu da zai kawo masu kudi.

“Shirin horaswar zai kula da turakun gwamnatinmu wanda su ne: Amfani da lmi da fasaha wajen maida Legas kasa daidai da zamanin nan.”

KU KARANTA: EndSARS: Shawarwarin da Gowon, Obasanjo, Jonathan su ka ba Gwamnati

Sanwo-Olu ya bayyana shirin daukar Matasa 400 da za koya wa sanin-aiki
Gwamna Sanwo-Olu Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kwamishinar ta ce: “Wadanda su ka yi dace za su rika samun abin kashe wa na N40, 000 na watanni shida da su ke daukar wannan horo.”

Masu bukata za su garzaya shafin gipplasg.lagosstate.gov.ng a yanar gizo. Dole sai mutum ya yi bautar kasa, kuma ya yi rajista da LASRRA.

A baya kuma kun ji cewa Kungiyar ASUU ta na zargin Gwamnatin Buhari da hana tattaunawarsu wajen kawo karshen yajin-aiki ya tafi sumul-sumul.

A cewar shugaban ASUU, har yanzu wamnati ba ta kama hanyar kawo karshen yajin-aikin ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel