An kona Masallatai har biyu a Jihar Enugu a dalilin rikici da Mai Keke Napep

An kona Masallatai har biyu a Jihar Enugu a dalilin rikici da Mai Keke Napep

- Rikici ya barke a garin Nsukka, Enugu, har ta kai an rusa Masallatai biyu

- Wasu mutane sun daba wa Direba wuka saboda sabani a kan kudin mota

- Hakan na zuwa ne bayan tsageru sun rusa babban masallacin Orlu a Imo

Makonni biyu da kona babban masallacin garin Orlu a jihar Imo, an sake kona wasu masallatan a jihar Enugu, Muslim News ta bada rahoto wannan.

Jaridar ta ce an kona wadannan masallatai ne a garin Nsukka, Enugu da ke Kudancin Najeriya.

Yayin da ‘yan kungiyar IPOB ne ake zargi da laifin kona masallacin garin Orlu, a jihar Enugu ana zargin wasu mutanen gari ne da wannan danyen aiki.

KU KARANTA: An tada bam cikin Masallaci a Borno j

Wannan lamari ya auku ne a ranar 31 ga watan Oktoba, 2020, an kada babban masallacin da ke kan titin Edem da kuma masallacin da ke hanyar bariki.

Duka wadannan dakunan ibada su na cikin garin Nsukka ne a jihar Enugu. An kona masallacin titin Edem kurmus, sannan aka rusa na hanyar barikin sojoji.

‘Yan kungiyar Keke Riders na direbobin Keke Napep ne da wasu matasa su ka taru su ka yi raga-raga da wadannan manyan masallatai biyu da ke jihar.

Fauziyat Ida Idoko ta gidauniyar Jaiz Foundation ta ce lamarin ya auku ne bayan an samu sabani tsakanin wata musulmar fasinja da direbobin keke napep.

KU KARANTA: Shugaba Donald Trump ba zai zarce kan mulkin Amurka ba – Hasashe

An kona Masallatai har biyu a Jihar Enugu a dalilin rikici da Mai Keke Napep
Masallatan Enugu Hoto: punchng.com/mosques-burnt-as-siblings-stab-enugu-tricycle-rider-over-fare
Asali: UGC

Wannan Baiwar Allah ta tare keke napep dauke da N150, inda aka fada mata cewa zata biya N250 kafin a kai ta inda za ta sauka, da aka isa sai ta bada N150.

A dalilinhaka rikici ya barke har ‘yanuwanta su ka zo, ana haka ne sai wani ya daba wa direba wuka. Nan take aka sheka da shi zuwa wani asibiti a Nsukka.

Daga nan ne aka zuzuta labarin ana cewa direban ya mutu. Wannan ya sa mutanen garin Enugu su ka rika kai wa musulmai hari, har aka kona masa masallatai.

Dazu kun ji cewa mazauna kauyen Takulashi da ke yankin Shikarkir, a karamar hukumar Chibok sun koka game da harin da 'Yan Boko Haram su ka kai masu.

'Yan ta'addan na Boko Haram sun kona kauye guda a jihar Borno bayan dakarun soji sun ki amsa kiran gaggawan da aka yi masu na zuwa su kawo doki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel