Yanzu-yanzu: An tayar da Bam cikin Masallaci a Borno

Yanzu-yanzu: An tayar da Bam cikin Masallaci a Borno

Yan kunar bakin wake biyu sun kai harin Bam cikin Masallaci a garin Gwoza, jihar Borno a ranar Lahadi inda yaro daya dan shekara 12 ya mutu yayinda mutane da dama suka jikkata.

Wani majiya daga gidan Soja, ya bayyana cewa yan kunar bakin waken sun ratsa cikin Masallaci yayinda ake cikin Sallah.

Kafin Masallatan su ankara, yaun kunar bakin waken sun shige cikin Masallacin.

Wannan harin ya faru ne a Guduf Nagadiyo da ke Bulabulin, Gwoza. Daga baya Sojojin bataliyan 192 suka isa wajen kuma suka yiwa Masallacin zobe.

Wani mazauni ya bayyana cewa da alamun yan kunar bakin waken sun shiga cikin garin ne ranar Asabar da aka gudanar da daurin aure a fadar sarkin Gwoza.

Yanzu-yanzu: An tayar da Bam cikin Masallaci a Borno
Yanzu-yanzu: An tayar da Bam cikin Masallaci a Borno
Asali: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa an shiga rudani a garin Mainok, dake babban hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a jihar Borno, bayan wasu Sojoji sun budewa jami'an yan sandan SARS da sukayi artabu da sukayi da yan Boko Haram.

Ofishin SARS sashe ne na hukumar yan sandan Najeriya da suka shahara da yakan yan fashi da makami.

Kauyukan da ke tsakanin Borno da Yobe na fuskantar barazana daga hannun yan Boko Haram tun da aka shiga sabuwar shekara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng