Mayakan Boko Haram sun kone kauye guda a Borno bayan dakarun soji sun ki amsa kiran gaggawa

Mayakan Boko Haram sun kone kauye guda a Borno bayan dakarun soji sun ki amsa kiran gaggawa

- Jama'a mazauna kauyen Takulashi da ke gundumar Shikarkir a karamar hukumar Chibok sun koka

- Sun bayyana yadda dakarun sojin sama suka yi burus da kiran gaggawa da aka yi musu a yayin da aka kai musu hari

- Majiyoyi a kauyen sun ce rayuka 11 sun salwanta kuma mayakan ta'addancin sun kone dukkan gidajen kauye

Dakarun sojin saman Najeriya basu dauka kiran da aka dinga musu ba domin su kawo dauki ga jama'ar kauyen Takulashi da ke gundumar Shikarkir a karamar hukumar Chibok ta jihar Borno, majiyoyi daga rundunar ta tabbatar wa The Cable.

Wurin karfe 10 na safiyar Lahadi, wasu mayakan ta'addanci sun tsinkayi kauyen inda suka dinga harbe-harbe sannan suka banka wa gidaje wuta.

Majiyoyi daga mazauna kauyen sun sanar da cewa a kalla rayuka 11 suka salwanta kafin zuwan dakarun da ke Chibok.

"Mayakan sun iso a motocin yaki shida, sauran ababen hawa uku da kuma miyagun makamai. Sun kashe wasu 'yan sa kai wadanda suka fara tunkararsu sannan suka kwace musu mota kirar Hilux," wata majiya tace.

"A lokacin da suka iso, shugaban 'yan sa kan ya gaggauta kira dakarun sojin. Daga bayanan da ya bada, sai dakarun sojin kasa suka fara neman tallafi daga sojin saman.

“Amma kuma abun takaici ba a samu tallafin daga dakarun sojin saman ba. An kone dukkan kauyen kuma bayan sa'a daya da aka yi musayar wuta, sai mayakan Boko Haram suka tsere," tace.

Wata majiya ta ce mayakan ta'addancin sun isa garin da yawansu amma da sojojin saman sun isa da wuri, da tuni sun ga bayan 'yan ta'addan.

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Ibikunle Daramola, ya bukaci da a tuntubi hedkwatar tsaro domin karin bayani.

KU KARANTA: 'Yan adawa ke daukar nauyin 'yan daba domin lalata mulkina - Gwamnan PDP ya koka

Mayakan Boko Haram sun kone kauye guda a Borno bayan dakarun soji sun ki amsa kiran gaggawa
Mayakan Boko Haram sun kone kauye guda a Borno bayan dakarun soji sun ki amsa kiran gaggawa. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matar aure nake bukata mai addini, da yanayi kadan na Nicki Minaj - Matashi

A wani labari na daban, rundunar sojin kasa ta ce ba za ta gabatar da sunayen jami'anta da aka tura Lekki Toll Gate ba, a ranar 20 ga watan Oktoban 2020, The Cable.

Faruwar al'amarin ya janyo hankalin mutanen ciki da wajen Najeriya, yayin da aka zargi sojoji da gwamnatin tarayya da tozarta hakkin bil'adama.

Duk da rahotanni na nuna an kashe mutane da dama, amma har yanzu kisan mutum daya kacal aka tabbatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel