Wani hazikin soja ya mutu yayin ceto mata masu shayarwa a Katsina

Wani hazikin soja ya mutu yayin ceto mata masu shayarwa a Katsina

- Rundunar Operation Sahel Sanity a jihar Katsina sun yi gagarumin nasara kan yan fashi

- Dakarun sun kuma yi nasarar ceto mata masu shayarwa su uku da yaransu

- Sai dai an rasa wani hazikin soja yayinda sojojin suka halaka yan bindiga uku

Dakarun sojoji Najeriya karkashin shirin Operation Sahel Sanity sun ragargaji yan fashi a jihar Katsina, inda suka yin nasarar ceto wasu mata masu shayarwa su uku da jariransu.

Har ila yau hazikan sojin sun yi nasarar halaka uku daga cikin yan ta’addan a musayar wuta da suka yi a ranar Alhamis da ta gabata, kamar yadda daraktan labarai na rundunar, Birgediya Janar Bernard Onyeuko ya fitar.

An tattaro cewa sojojin sun kar doki ne bayan samun bayanai cewa yan fashin sun kai farmaki a kauyen Diskuru da ke karamar hukumar Faskari da misalin karfe 5:30 na asuba.

Sun kai farmakin ne a kan Babura, inda suka halaka mutane da dama.

Dakarun rundunar sun yi nasarar dakile harin tare da raunata da yawa daga cikin miyagun.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Ba za mu tilasta wa kowani jami’in dan sanda komawa bakin aiki ba –Hukumar yan sanda

Wani hazikin soja ya mutu yayin ceto mata masu shayarwa a Katsina
Wani hazikin soja ya mutu yayin ceto mata masu shayarwa a Katsina Hoto: WazupNigeria
Asali: UGC

"Bayan fafatawar, an ceto mata tare da yaransu waɗanda 'yan fashi suka yi garkuwa da su," in ji Bernard Onyeuko.

An gano karin gawawwaki biyu na 'yan fashi biyu a kan hanyarsu ta guduwa, a cewarsa.

Sai dai ya ce wani soja da ya yi koƙarin tserar da ɗaya daga cikin matan da aka yi garkuwar da su ya rasa ransa yayin fafatawar, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Sojojin sun ci gaba da kasancewa a garin bayan korar 'yan fashin domin tabbatar da tsaro a yankin da kuma makwabtansa.

KU KARANTA KUMA: Mun yarda mun kasa taɓuka komai wa yaran Nigeria - Ministar kuɗi

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Isah Gambo, ya tabbatar da cewa mutum 17 ne suka mutu jumulla. Hudu daga cikinsu dakarun sa-kai ne, da 12 kuma mazauna kauyen ne.

A wani labarin, mun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta tura tawagar mata zalla zuwa jihar Anambra domin aikin kiyaye zaman lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel